An harbi DPO, an kashe mutane 5, an sace shugaban karamar hukuma a Katsina

An harbi DPO, an kashe mutane 5, an sace shugaban karamar hukuma a Katsina

Wasu hare - hare da aka kai a kananan hukumomin Faskari da Sabuwa a jihar Katsina sun yi sanadiyyar mutuwar mutane biyar.

An harbi shugaban 'yan sanda na karamar hukuma, ACP Aminu Abdulkarim, tare da yin awon gaba da shugaban karamar hukumar Danmusa, Yahaya Musa Sabuwa.

Da ya ke tabbatar da faruwar lamarin, gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya ce, "jihar Katsina na fuskantar hare - hare daga wasu 'yan bindiga da su ka ki tuba har yanzu.

"Mu na cikin mawuyacin hali, ba cutar coronavirus ce matsalar wasu sassan jihar Katsina ba, cutar 'yan bindiga ne matsalar.

"Kiris ya rage a kashe DPO na karamar hukumar Faskari, yanzu haka ya na can asibiti a kwance. Mu na fatan zai tsira da ransa.

"Wasu 'yan bindiga sun kai hari wani kauye a karamar hukumar Sabuwa, inda su ka kashe mutane biyar tare da sace mu su dukkan dabbobinsu.

An harbi DPO, an kashe mutane 5, an sace shugaban karamar hukuma a Katsina
Aminu Masari
Asali: UGC

"A daren ne wasu 'yan bindiga kusan su 100 su ka dira gidan shugaban karamar hukumar Danmusa, wanda dan asalin karamar hukumar Sabuwa ne, su ka sace shi tare da dansa."

DUBA WANNAN: Mutane 156 sun mutu a cikin kwana 6 a kananan hukumomi biyu a Yobe

Masari ya bayyana cewa 'yan bindiga sun kashe mutane 50 a cikin sati biyu, sannan ya kara da cewa, "kusan kullum sai an kai hari a wani bangare na jihar Katsina. Jami'in da ke kawo min rahoto har nauyi ya ke ji ya kalli fuskata ya sanar da ni cewa an kai hari a wani gari.

"Mazauna garin Faskari sun yi barazanar daukan makamai domin kare kansu, amma na roki shugabannin siyasa na yankin a kan su rarrashesu, saboda sun hada kansu tare da yin shirin fita koda za a kashesu."

Gwamna Masari ya ce 'yan bindigar sun mallaki manyan makamai tare da yin kira ga jami'an tsaro da su kara himma wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyar jama'a a jihar Katsina.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng