A karon farko: An yanke wa wani mutum hukuncin kisa ta yanar gizo a Najeriya

A karon farko: An yanke wa wani mutum hukuncin kisa ta yanar gizo a Najeriya

- Wata kotun Najeriya ta yankewa wani mai laifi hukuncin kisa ta hanyar rataya ta yanar gizo

- Kamar yadda jaridar The Nation ta bayyana, Mai shari'a Mojisola ya kama Olalekan Hameed da laifin kisan kai

- Saii dai, kungiyar rajin kare hakkin dan Adam ta soki hukuncin amma ta yi maraba da salon shari'ar ta yanar gizo

Wata kotun Najeriya da ke shari'a ta yanar gizo ta yanke wa wani mutum hukuncin kisa ta hanyar rataya.

An yi shari'ar ta yanar gizo ne bayan gwamnati ta rufe kotuna don gudun ci gaban yaduwar annobar korona.

Mutumin mai sun Olalekan Hameed ya samu wannan hukuncin ne a zaman kotun da aka gudanar ta kafar bidiyon a Zoom.

Mai shari'a Mojisola Dada ne ya tabbatar da zartar da hukuncin kisa ta hanyar ratayar a kan Olalekan Hameed.

An tabbatar da cewa mai laifin ya kashe mahaifiyar mai gidansa da yake yi wa aikin direba.

A halin yanzu, masu rajin kare hakkin bil Adama sun soki hukuncin. Amma kuma sun yi maraba da sabon salon shari'ar ta yanar gizo saboda annobar korona.

A karon farko: An yanke wa wani mutum hukuncin kisa ta yanar gizo a Najeriya

A karon farko: An yanke wa wani mutum hukuncin kisa ta yanar gizo a Najeriya. Hoto daga BBC
Source: Getty Images

KU KARANTA: Yadda aka yi wa kwarto dukan kisa

A wani labari na daban, wani mutum mai suna Timothy Osai mai shekaru 34 ya sha mugun duka wanda ya yi sanadin mutuwarsa.

Ana zargin Osai ne da kwartanci da matar wani mai sarauta a Ihie, karamar hukumar Ohaji-Egbema da ke jihar Imo, jaridar The Nation ta wallafa.

An gano cewa wadanda suka kashe shi din hayarsu aka yi, kamar yadda jaridar The Nation ta wallafa. Osai ya mutu ne sakamakon raunikan da ya samu bayan ya sha muguwar jibga.

Lamarin ya faru ne a ranakun karshen makon da suka gabata. An gano cewa Osai na mu'amala da matar auren wacce dan uwan shi ya ja masa kunne a kan hakan.

Bai ji jan kunnen ba, lamarin da yasa aka kira mishi 'yan kungiyar sirri wadanda suka aika shi lahira.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel