Na zabi a ba ‘Yaradua kyautar zaman lafiya na Duniya a 2010 - Ekweremadu

Na zabi a ba ‘Yaradua kyautar zaman lafiya na Duniya a 2010 - Ekweremadu

- Sanata Ike Ekweremadu ya ce Najeriya ta yi rashin Shugaba Ummaru ‘Yar’adua

- ‘Dan majalisar ya fadi abin da ya sa ya zabi a ba ‘Yar'adua kyautar ‘Nobel’ a 2010

- ‘Yaradua ya yi kokari wajen kawo zaman lafiya a Neja-Delta mai arzikin man fetur

Yayin da ake makokin shekara goma da rasuwar marigayi Alhaji Ummaru ‘Yar’adua, fitaccen sanatan jam’iyyar PDP, Ike Ekweremadu ya yi magana game da tsohon shugaban kasar.

Sanata Ike Ekweremadu ya ce: “Mun rasa shugaba (Ummaru Musa) ‘Yar’adua shekaru goma da su ka wuce. A Yulin 2007, na jagoranci sanatocin kudu maso gabas mu ka gana da shi.”

Sanatocin sun kokawa ‘Yar’adua cewa ba su da babban filin jirgi. Wannan ganawa da shugaban ta yi sanadiyyar gyara filin tashi da saukar jirgin sama na Akanu Ibiam da ke garin Enugu.

Bayan taimakawa yankin kudu maso gabashin Najeriya da hanyar da za su rika fita kasashen waje kai tsaye, ya ce gwamnatin ‘Yar’adua ta yi kokarin kawo karshen rikicin Neja-Delta.

KU KARANTA: Abin da mutane ke cewa game da ‘Yar’adua bayan shekaru 10 da rasuwa

“Ya rubuta sunansa da ruwan zinari a tarihi da ya kirkiri ma’aikatar Neja-Delta a 2008, sannan kuma ya kulla yarjejeniya da tsageru a 2009 domin samun zaman lafiya da tsaro a yankin.”

“Sai da na zabe shi domin a ba shi kyautar zaman lafiya na Duniya a 2010. Bai yi nasarar lashe kyautar ba, amma Duniya ta san cewa shi adali ne kuma mai neman zaman lafiya." Inji sa.

‘Dan majalisar ya karkare da yi wa tsohon shugaban addu’a, ya na cewa: “Allah ya cigaba da yi masa rahama, kuma ya karbi bakuncinsa.” Ekweremadu ya rubuta wannan ne a Tuwita.

Legit.ng za ta tuna cewa a shekarar 2010, Liu Xiaobo ne ya yi nasarar lashe wannan kyauta ta Duniya sakamakon irin gwagwarmayar da ya yi wajen kare hakkin Bil Adama a kasar Sin.

Ekweremadu ya rike kujerar mataimakin shugaban majalisar dattawa na tsawon shekara 12. Sauran manyan kasa irinsu Bukola Saraki, Atiku Abubakar duk sun tuna da 'Yar'adua jiya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel