Mun karbi wasu gudumuwar kudin da aka bada na yaki da COVID-19 inji SGF
Gwamnatin Najeriya ta yi magana game da gudumuwar da attajirai da manyan masu hali su ka bada domin a yaki annobar cutar Coronavirus da ta addabi kasashen Duniya da dama.
Sakataren gwamnatin tarayya, Mista Boss Mustapha wanda shi ne shugaban kwamitin da shugaba Muhammadu Buhari ya kafa domin yaki da COVID-19 ya bayyana inda aka kwana.
Boss Mustapha ya halarci wani zama da aka yi a majalisa tare da sauran ‘yan kwamitinsa, ya kuma tabbatar cewa wadannan gudumuwa da aka bada sun fara shigowa hannun gwamnati.
Ministan lafiya, Dr. Osagie Enahire da shugaban NCDC mai takaita yaduwar cututtuka a Najeriya, Dr. Chikwe Ihekweazu su na cikin sauran ‘yan kwamitin da su ka halarci zaman majalisar.
‘Yan majalisa sun yi wa kwamitin PTF tambayoyi game da nasarorin da ake samu wajen yaki da annobar Coronavirus. Daga cikin tambayoyin da aka yi wa kwamitin har da batun gudumuwa.
KU KARANTA: ‘Yan Majalisa za su binciki kan zargin badakala a Hukumar NDDC
Shugaban majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila ya tambayi shugaban kwamitin na PTF ko duk gudumuwar da jama’a su ka bada ya iso hannunsu, kwamitin ya kudin sun fara shigowa.
Mustapha ya ce gudumuwar da ake badawa su na zuwa cikin wani asusu na musamman ne da ke babban bankin Najeriya na CBN. Kwamitin ya ce a nan ake tara duk wasu kudin da aka samu.
Kamar yadda majalisar wakilan ta bayyana a shafin ta na Tuwita jiya, kwamitin da ke yaki da cutar COVID-19 a kasar bai bayyana adadin gudumuwar da su ka samu wajen Bayin Allah ba.
Bayan haka kuma ‘yan majalisa sun tambayi kwamitin game da batun biyan ma’aikatan lafiya alawus na musamman a lokacin wannan annoba, a nan ma PTF ta ce ana biyan alawus.
PTF ya ce alawus din da ake biyan malaman da ke aikin kula da masu jinyar COVID-19 a asibiti ya danganta ne daga jiha zuwa jiha, shugaban kwamitin ya ce ba a kayyade alawus din ba.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng