Shugaban NNL kuma mamba a FA ya fadi, ya mutu a take

Shugaban NNL kuma mamba a FA ya fadi, ya mutu a take

Mamba a kwamitin kungiyar kwallon kafa ta Najeriya kuma shugaban Nigeria National League, Chidi Ofo-Okenwa, ya rasu yana da shekaru 50 a duniya.

An tabbatar da hakan ne daga bakin mai magana da yawun NFF, Ademola Olajire a wata takardar da ya fitar a yau Talata.

Jaridar The Punch ta gano cewa Ofo-Okenwa wanda ya rasu da safiyar yau Talata, ya kasa bacci ne tun a daren Litinin.

A takardar da Olajire ya fitar, ya ce an yi duk kokarin da za a iya don tseratar da rayuwar shugaban kungiyar kwallon kafan bayan ya fadi da safiyar Talatar, amma abin ya ci tura.

Shugaban NNL kuma mamba a FA ya fadi, ya mutu a take
Shugaban NNL kuma mamba a FA ya fadi, ya mutu a take
Asali: UGC

Ya ce, “Okenwa, wanda shine shugaban kungiyar kwallon kafa ta jihar Enugu an gano yana fama da cutar sankarar jini. Ya kasa bacci cikin dare kafin da safe ya fadi.

“An gaggauta kai shi asibiti mai zaman kansa a jihar Enugu amma sai aka tabbatar da cewa ya rasu.

“An adana gawar Chidi Ofo Okenwa a ma’adanar gawawwaki da ke asibitin kuma an tuntubi iyalansa a kan yadda za a birnesa.”

Shugaban kungiyar kwallon kafa ta Najeriya, Amaju Pinnick, ya jajanta rasuwar shugaban wanda ya rasu bayan kwanaki 10 da cikarsa shekaru 50.

Pinnick ya kara da cewa, “Wannan al’amari ya matukar girgiza kowa kuma NFF na cikin alhini. Chidi ma’aikaci ne mai matukar biyayya kuma yana kan gaba a kungiyar. Wannan babban rashi ne.

KU KARANTA KUMA: An bayyana muhimman aiyuka 2 da kudin Abacha za su iya kammalawa a Najeriya

“Mutum ne da a koda yaushe za ka iya neman shawararsa. Muna hada hikimomi da shawarwari tare da fitar da wadanda za su amfanemu saboda gogewarsa da ilimi. Mun yi babban rashi.”

A wani labarin kuma, mun ji cewa hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa (NEMA) ta sanar da mutuwar Saidu Ahmed, shugabanta na yankin arewa maso gabas.

Abdulkadir Ibrahim, shugaban sashen yada labarai na NEMA a yankin arewa maso gabas, ne sanar da mutuwar Ahmed yayin ganawarsa da kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) a Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Ibrahim ya ce shugaban ya mutu ne ya asibitin koyarwa na jami'ar Maiduguri (UMTH) bayan ya sha fama da ciwon sukari.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel