Yawo da Almajirai tsakanin Jihohi ya ci karo da doka - Sakataren Gwamnati

Yawo da Almajirai tsakanin Jihohi ya ci karo da doka - Sakataren Gwamnati

- Sakataren gwamnatin tarayya ya soki yadda ake yawo da Almajirai daga Jiha zuwa Jiha

- Shugaban kwamitin yaki da COVID-19 a Najeriya ya ce wannan aiki ya ci karo da dokoki

Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha wanda shi ne shugaban kwamitin shugaban kasa na yaki da COVID-19 a Najeriya ya yi magana game da yawo da almajirai da ake yi.

SGF ya ce yawan yawo da almajirai da ake yi bini-bini daga wannan jiha zuwa wannan, ba ya kan tsarin sharudan da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gindaya na tafiye-tafiye.

Boss Mustapha ya ce har zuwa Lahadi ana yawo da almajirai tsakanin jiha zuwa wata, wanda ya ce wannan ya ci karo da dokar da shugaban kasa ya sa na haramta shiga wata jiha.

Shugaban kwamitin yi wannan kuka ne a ranar Litinin, 4 ga watan Mayu, wajen wani taro da PTF ta shirya a Abuja. Ya ce kwamitin PTF za ta gana da jihohin kasar.

KU KARANTA: Kusan 85% na masu dauke da COVID-19 a jihar Kaduna Almajirai ne

Ya bayyana cewa za su yi wani zama da gwamnonin jihohi domin su nuna masu yadda za a cin ma bukatun kwamitin shugaban kasar wajen hana yaduwar cutar Coronavirus.

“PTF ta samu rahoto game da bin dokar da shugaban kasa ya sa na haramta tafiya daga wata jiha zuwa wata a Najeriya. Manufar dokar ita ce a rage yaduwar COVID-19 ta iyakokin jihohi.”

“Ana samun labarin daukar almajirai daga wannan jihar zuwa wannan har zuwa jiya (Lahadi), a yayin da dokar haramcin ta ke kasa, cigaba da yin wannan aiki ba ya kan tsari.” Inji Shi

Domin ganin an yi maganin wannan lamari, Mista Boss Mustapha ya kara da cewa: “Kwamitin PTF za ta zauna da wadannan gwamnatocin jihohi a kan yadda za ta cin ma manufofinta.”

Jaridar Daily Trust ta ce kusan duk gwamnonin Arewa ne suke ta wannan kokari na maida almajirai jihohin da su ka fito. Gwamnonin sun ce hakan zai taimaka ayi yaki da COVID-19.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Online view pixel