Tsohon hadimin marigayi Yar'adua ya mutu a Kano

Tsohon hadimin marigayi Yar'adua ya mutu a Kano

Rabi'u Musa, sakataren yada labarai na tsohon shugaban kasa Umaru Musa Yar'adua ya rasu.

Musa ya rasu yana da shekaru 60 a duniya kamar yadda jaridar Premium Times ta wallafa.

Musa ne tsohon sakataren yada labarai na Yar'adu a yayin da yake gwamnan jihar Katsina.

Kafin rasuwarsa, shine shugaban fannin sadarwa na ofishin UNICEF a jihar Kano.

Dan sa mai suna Musa Rabiu ne ya sanar da rasuwarsa ga jaridar Premium Times. Ya rasu ne bayan gajeriyar rashin lafiya a ranar Asabar.

Tsohon hadimin marigayi Yar'adua ya mutu a Kano

Tsohon hadimin marigayi Yar'adua ya mutu a Kano
Source: UGC

Ya ce marigayin ya cika ne wurin karfe 3 na dare a ranar Asabar bayan ya yi kwanaki kadan yana jinya a asibitin kashi na Dala da ke Kano.

Ya rasu ne a yayin da ake jiran sakamakon gwajin cutar coronavirus da aka yi mishi bayan ya bayyana da alamun cutar.

"Mako daya da ya gabata, ya fara korafin mura da cutar zazzabin cizon sauro amma sai ya warke. Ya fara korafin sarkewar numfashi daga bisani," dan sa ya sanar.

Ana ci gaba da samu hauhawar yaduwar cutar coronavirus a jihar Kano tun a makonni biyu da suka gabata tare da yawaitar mace-mace.

KU KARANTA KUMA: Abba Kyari bai taba tuka mota ba har zuwa mutuwarsa, in ji diyarsa

A halin yanzu jihar ce ke biye da Legas a yawan mutanen da suka kamu da cutar a fadin kasar nan.

A wani labari na daban, mun ji cewa kimanin sati biyu da suka gabata, gwamnatin jihar Katsina ta sanar da rufe karamar hukumar Daura biyo bayan mutuwar wani mai dauke da kwayar cutar covid-19.

A wani labari da jaridar Daily Trust ta wallafa a yau, Litinin, 04 ga watan Mayu, ta bayyana cewa an rufe fadar masarautar Daura bayan samun bullar annobar covid-19.

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, dan asalin karamar hukumar Daura ne.

Sakataren gwamnatin jihar Katsina, Dakta Mustapha Inuwa, ya tabbatar da rufe fadar sarkin tare da bayyana cewa sakamakon gwajin da ake jira ne kadai zai nuna lokacin da za a bude fadar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel