Ya kamata CBN ya rage adadin ruwa a bashi domin a samu aikin yi - Tinubu

Ya kamata CBN ya rage adadin ruwa a bashi domin a samu aikin yi - Tinubu

Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya yi kira ga gwamnatin tarayya da babban bankin Najeriya su yi amfani da damar da tattalin arzikin kasa ta shiga ciki a lokacin annobar COVID-19.

Babban jagoran na jam’iyyar APC ya fitar da wani dogon jawabi ya na mai kira a rage kason ruwa daga cikin bashin banki. ‘Dan siyasar ya fitar da wannan jawabi ne a ranar Lahadi.

Bola Tinubu ya ce akwai bukatar CBN ya rage adadin ruwa a bashi domin mutane su samu damar cin bashi da kuma yin kasuwanci a cikin gida maimakon shigo da kaya daga waje.

Tsohon gwamnan Legas, Bola Ahmed Tinubu ya ce an samu makekiyar tazara tsakanin bukatu da samar da kaya a kasuwa ne saboda tsadan ruwa da farashin kudin kasashen waje.

Tinubu ya bada shawarar cewa rage ruwan da ke kan bashi zai zaburar da tattalin arziki ta hanyar kirkiro da ayyukan yi da samar da dukiya da za ta rika yawo sosai cikin jama'a.

KU KARANTA: Tattalin arziki: APC ta karbi shawarar da Atiku ya ba Shugaba Buhari

Duk da alherin rage ruwan da ke kan bashin banki, Tinubu ya yarda cewa yin hakan zai sa farashin kaya su tashi a kasuwa. Sai dai a karshe ya ce za a ji dadin tattalin arzikin kasar.

“Matsayata tun tuni ita ce ina da ja game da cin bashin kasar waje saboda wahala wajen biya. Amma idan mu na bukatar kudin waje domin sayo muhimman kaya, yanzu ne lokacin haka.”

“Domin zaburar da tattali, manyan bankunan kasashen da tattalin arzikinsu ya bunkasa su na ta rage ruwan da ke kan bashi zuwa kasa da 1% ko kuma kusan 0%." Inji jigon na APC mai mulki.

Tinubu ya ke cewa ana bada aron kudi domin tallafawa kasuwanci da kamfanonin 'yan kasa. Tinubu ya nemi Najeriya ta yi amfani da wannan dama ta sake zama da manyan Duniya.

“Bankin Duniya da sauran masu bada tallafi sun ce za su bada aron kudi cikin rahusa. Mu nemi a sake duba yarjejeniyar bashin da mu ka ci, ko mu nemi a yafe mana aron da mu ka karba.”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel