Jama’a su na kaffa-kaffa da Jihar Kano yayin da Coronavirus ta ke kara ta’adi

Jama’a su na kaffa-kaffa da Jihar Kano yayin da Coronavirus ta ke kara ta’adi

Rahotanni su na zuwa mana cewa an shiga cikin wani irin hali a jihar Kano, inda ta kai Bayin Allah su na barin gari a sakamakon yawan mace-macen da ake samu a kwanakin nan.

Jaridar This Day ta fitar da wani dagon rahoto ta na cewa mutane su na kaura daga Kano, kuma akwai yiwuwar a sanadiyyar haka an yada cutar COVID-19 a jihohin da ke kusa da Kano.

Ganin halin da aka shiga ciki ne gwamnatin tarayya ta bude wasu sababbin dakunan gwaji uku a jihar Kano domin a shawo kan annobar Coronavirus da ake zargin ta kashe dinbin mutane.

A karshen makon nan ne mai martaba Sarkin Rano, Alhaji Tafida Abubakar Ila ya cika. Haka kuma an samu labarin mutuwar wani babban jami’in hukumar UNICEF, Rabiu Musa a jiya.

Kawo yanzu ba a iya tabbatar da ainihin abin da ke kashe mutane rututu a jihar Kano ba. Hakan ya bayu ne da cewa musulmai su kan bizne gawansu ne ba tare da sun bata wani lokaci ba.

KU KARANTA: An samu wasu Almajirai da su ka fito daga Kano da ke dauke da COVID-19

A ranar Asabar an samu sauki a Kano, inda hukumar NCDC ta ce mutane uku kawai aka samu dauke da cutar COVID-19. A daidai wannan lokaci gwamnati ta na ganin cewa za a kai ga ci.

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya na cikin masu kira da babbar murya cewa dole sai an hada-kai wajen takaita yaduwar Coronavirus a Kano idan ana so a ceci kasar.

Sanata Shehu Sani, tsohon shugaban hukumar NHIS, Farfesa Usman Yusuf, da tsohon gwamnan Kano duk sun yi irin wannan kira da gwamnati ta ke ganin akwai burbushin siyasa a ciki.

Mawakbtan Kano irinsu Kaduna su na zargin almajiran da su ka fito daga jihar su na kawo masu cutar COVID-19. Gwamnatin Kano ta maida wasu almajirai zuwa garuruwan da su ka fito.

Bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada umarni rufe Kano, gwamna Abdullahi Ganduje ya fito ya sassauta takunkumin, ya ayyana ranakun da jama’a za su rika zuwa kasuwa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel