Covid-19: Sabbin mutane 220 sun kamu, 11 sun mutu a Borno, ta lafa a Kano

Covid-19: Sabbin mutane 220 sun kamu, 11 sun mutu a Borno, ta lafa a Kano

A cikin sanarwar da NCDC ta saba fitarwa kusan 12:00 na daren kowacce rana a shafinta na tuwita, ta sanar da cewa karin sabbin mutane 220 ne aka tabbatar da cewa kwayar cutar covid-19 ta harba a fadin Najeriya.

Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da NCDC ta fitar da misalin karfe 11:56 na daren ranar Asabar, 02 ga watan Mayu, 2020.

NCDC ta fitar da jerin jihohi da jimillar ma su dauke da kwayar cutar a kowacce jiha kamar haka;

62-Lagos

52-FCT

31-Kaduna

13-Sokoto

10-Kebbi

9-Yobe

6-Borno

5-Edo

5-Bauchi

4-Gombe

4-Enugu

4-Oyo

3-Zamfara

2-Nasarawa

2-Osun

2-Ebonyi

2-Kwara

2-Kano

2-Plateau

NCDC ta ce ya zuwa karfe 11:50 na daren ranar Asabar, 02 ga watan Mayu, akwai jimillar mutane 2388 da aka tabbatar da cewa suna dauke da kwayar cutar covid-19 a Najeriya.

An sallami mutane 385 bayan an tabbatar da samun saukinsu, a yayin da cutar ta hallaka jimillar mutane 85.

DUBA WANNAN: Covid-19: Ku fidda ran daidaituwar al'amura a cikin shekarar nan - Shugaban NCDC

An samu jimillar mutane 69 da aka tabbatar da cewa suna dauke da kwayar cutar covid-19 a jihar Borno.

Daga cikin jimillar mutane akwai ma'aikatan lafiya 16 da su ka kamu da kwayar cutar yayin aikin taimakon masu jinyarta a jihar Borno.

Kazalika, annobar ta yi sanadiyyar mutuwa mutane 11 a jihar Borno.

Usman Umar kadafur, mataimakin gwamnan jihar Borno, sannan shugaban kwamitin kar ta kwana a kan annobar covid-19, ne ya sanar da hakan ranar Asabar yayin da ya ke ganawa da 'yan jarida a Maiduguri.

A yayin da ya ke gabatar da nasa jawabin, kwamshinan lafiya a jihar Borno, Aliyu Salisu Kwaya Bura, ya bayyana dalilin karuwar adadin mutanen da annobar ke hallakawa a jihar Borno.

A cewarsa, kwayar cutar covid-19 ta fi saurin hallaka mutanen da ke fama da wasu cututtuka kamar asma, nimoniya, masassara, ciwon sukari, tayifod, da ciwon koda.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel