COVID-19: Dattawan arewa sun jinjinawa Buhari kan shiga cikin lamarin Kano da ya yi

COVID-19: Dattawan arewa sun jinjinawa Buhari kan shiga cikin lamarin Kano da ya yi

Kungiyar dattawan Arewa ta jinjinawa kokarin gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari, kan yadda ta dauka mataki a kan al'amarin da ke faruwa a jihar Kano.

Shugaban kungiyar, Farfesa Ango Abdullahi ya sanar da wannan jinjinar a Kaduna a ranar Alhamis, 30 ga watan Afrilu.

Abdullahi ya ce wannan matakin da gwamnatin tarayyar ta dauka zai taka rawar gani wajen hana yaduwar cutar a Arewacin Najeriya da kasar baki daya.

Kamar yadda yace, kungiyar ta matukar shiga damuwa a kan yaduwar Covid-19 a fadin kasar nan, jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

COVID-19: Dattawan arewa sun jinjinawa Buhari kan shiga cikin lamarin Kano da ya yi
COVID-19: Dattawan arewa sun jinjinawa Buhari kan shiga cikin lamarin Kano da ya yi
Asali: Facebook

"Kungiyar na jajantawa ga wadanda suka yi rashi sakamakon wannan annobar tare da fatan samun sauki ga wadanda ke jinya.

"Kungiyar ta jinjinawa kokarin gwamnatin tarayya ta yadda ta dauka mataki a kan halin da jihar Kano ta shiga. Hakan kuwa zai taka rawar gani wurin hana yaduwar cutar a arewa da kasar baki daya.

"Mun jinjina yadda aka tura kwararrun masana kiwon lafiya jihar don bincikar mace-macen da ke aukuwa wanda ake alakantawa da annobar."

Abdullahi ya yaba wa gwamnatin tarayya ta yadda za ta samar da kayan aiki tare da kayan bukata a madadin gwamnatin jihar Kano. Yayi fatan tallafin ya isa da gaggawa.

Amma kuma ya yi kira da babbar murya a kan cewa gwamnatin tarayya ta kara kokari wajen samar da kayan kariya don samun nasarar wannan yakin.

"Wadanda ke fama da wani rashin lafiya da ba annobar ba basu samun kulawa saboda rashin kayan aiki da ma'aikata.

KU KARANTA KUMA: An kama mutumin da ya fallasa jawabin shugaba Buhari – Femi Adesina

"Saurin samar da dakin gwaji da cibiyoyin killacewa bai kai yadda cutar ke yaduwa ba. Ya kamata gwamnatin jihar Kano tare da masu ruwa da tsaki su dauka matakin gaggawa," in ji Ango.

Abdullahi ya ce abin takaici ne yadda gwamnatocin wasu jihohi ke siyasantar da barkewar cutar.

A wani labarin kuma, mun ji cewa Gwamnan jahar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana dalilan da suka sa yake rokon gwamnatin shugaba Buhari ta sassauta ma jama’an Kano dokar hana fita da ta kakaba musu.

Daily Nigerian ta ruwaito a ranar Alhamis ne Ganduje ya yi wannan kira yayin da yake rantsar da wani kwamitin kwararru da za su taimaka ma kwamitin yaki da COVID19 na jahar Kano.

A jawabinsa, Ganduje ya roki Buhari ya rage kwanaki 14 da ya sanya ma jahar Kano na ba shiga ba fita, saboda a cewarsa hakan zai rage wahalhalu a jahar, musamman a watan Ramadan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel