Yanzu Yanzu: Allah ya yi wa wani dan majalisar dokokin jahar Nasarawa rasuwa

Yanzu Yanzu: Allah ya yi wa wani dan majalisar dokokin jahar Nasarawa rasuwa

- Dan majalisa mai wakiltan Nasarawa ta tsakiya a majalisar dokokin jahar Nasarawa, Alhaji Suleiman Adamu ya rasu

- Ya rasu ne a daren ranar Alhamis, 30 ga watan Afrilu bayan dan rashin lafiya

- Marigayin ya mutu ya bar matar aure daya da yara biyar

Allah ya yi wa wani mamba a majalisar dokokin jahar Nasarawa, Alhaji Suleiman Adamu rasuwa. Ya kasance mamba mai wakiltan Nasarawa ta tsakiya a majalisar jahar.

Mamba mai wakiltan mazabar Udege/Loko, Alhaji Mohammed Okpoku, ne ya sanar da batun mutuwar dan majalisar ga manema labarai a ranar Juma’a, 1 ga watan Mayu a karamar hukumar Nasarawa.

Kopoku ya bayyana cewa Suleiman ya rasu a daren ranar Alhamis, 30 ga watan Afrilu, bayan fama da dan rashin lafiya a cibiyar lafiya ta tarayya da ke Keffi.

Yanzu Yanzu: Allah ya yi wa wani dan majalisar dokokin jahar Nasarawa rasuwa

Yanzu Yanzu: Allah ya yi wa wani dan majalisar dokokin jahar Nasarawa rasuwa
Source: UGC

Ya bayyana cewa za a binne gawar dan majalisar da karfe 9:00 na safiyar ranar Juma’a a karamar hukumar Nasarawa.

“Ina bakin cikin sanar da mutuwar takwarana, Hon Suleiman Adamu, wanda muka fito daga karamar hukuma guda.

“Mutuwarsa ta kasance babbar rashi a garemu kuma za mu ci gaba da yi masa addu’ar samun jin kai,” in ji shi.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa marigayin ya mutu ya bar matar aure daya da yara biyar.

KU KARANTA KUMA: Allah ya yi wa jarumin Kannywood Ubale Ibrahim rasuwa

A wani labari na daban, mun ji cewa shugaban kwamitin shugaban kasa dake yaki da annobar COVID-19, wanda aka fi sani Coronavirus, Dakta Sani Aliyu ya rasa mahaifinsa, Alhaji Aliyu Daneji.

Jaridar Punch ta ruwaito Alhaji Daneji ya rasu ne a daren Laraba a jahar Kano yana da shekara 96 a duniya.

Guda daga cikin yayansa, Mahmud Daneji ne ya tabbatar da mutuwar mahaifin nasu, ina yace marigayim ya rasu ne bayan fama da jinya na dan karamin lokaci.

Da safiyar Alhami, 30 ga watan Afrilu aka gudanar da jana’izarsa a Sabuwar Kofa dake kusa da makarantar Firamari ta Kwalli, cikin birnin Kano, daga nan kuma aka binne shi.

Marigayi Aliyu Daneji ya taba zama babban sakatare a ma’aikatar kudi ta jahar Kano daga shekarar 1972 zuwa shekarar 1975.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel