Covid-19: Hukuma ta shiga neman wata mai jego ruwa a jallo bayan sakamakon gwajinta ya fito

Covid-19: Hukuma ta shiga neman wata mai jego ruwa a jallo bayan sakamakon gwajinta ya fito

Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki ya bayyana cewa ana neman wata mai jego mai suna Amaka Okoro, ido rufe a jihar.

Bayan an tabbatar da tana dauke da cutar coronavirus, ta tsere sannan an kasa gano inda take har yanzu.

"Wata mata mai suna Amaka Okoro ta tabbata dauke da cutar coronavirus kuma ana neman ta ido rufe don fara karbar magani.

"Tana da goyon yarinya wacce har ta fara tari. Tana zama ne a gida mai lamba 2, titin Idubor kusa da Ugbor a Benin City," cewar gwamnan.

Covid-19: Hukuma ta shiga neman wata mai jego ruwa a jallo bayan sakamakon gwajinta ya fito

Covid-19: Hukuma ta shiga neman wata mai jego ruwa a jallo bayan sakamakon gwajinta ya fito
Source: Twitter

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta bayyana, gwamnan yace, "Okoro a halin yanzu babban kalubale ce ga kanta, diyar da take goyo da kuma jama'a baki daya. Duk wanda ya san inda take, ya tuntubi hukumomi ko jami'an tsaro."

Obaseki ya kara da tabbatar da cewa wa'adin dokar hana zirga-zirga ta jihar ya karu da kwanaki 14.

Wasu mutane 20,000 na jihar an yi musu gwajin amma sakamakon 297 ne daga ciki ya bayyana.

Gwamnatin jihar Edo din ta amince da kara wa likitoci alawus din hatsarin da suke fuskanta daga N90,000 zuwa N300,000.

KU KARANTA KUMA: Cutar Coronavirus ta kashe dan shekara 25 a Lagas

A gefe guda, gidauniyar basarake Oba Ewuare ta bai wa kungiyar 'yan jaridun jihar Edo tallafi.

Tallafin ya hada da buhunan wake 50, buhunanan shinkafa 50, kwalin Indomie 50, takunkumin fuska 50 da sinadarin tsaftace hannu 50.

Obasogie na Benin, Eduwu Ekharor Obasogie ne ya gabatar da kayayyakin a madadin basaraken.

Ya ce wannan tallafin na daga cikin kokarin rage radadin kalubalen da ake fuskanta ne a yayin da aka rufe jihohi a kasar nan.

A wani labarin kuma, mun ji cewa Gwamnatin Jihar Zamfara ta ce tana neman wani Jamilu Shinkafi ruwa a jallo saboda tsere wa da ya yi bayan an masa gwaji an kuma gano yana dauke da kwayar cutar coronavirus.

Kwamishinan Lafiya na jihar, Yahaya Kanoma ya shaidawa The Punch cewa Shinkafi ya tsere bayan an tabbatar yana dauke da cutar da coronavirus.

Ya ce an tsananta bincike domin gano inda ya shiga ya boye.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel