Mace-macen Kano: Kashi 41 cikin 100 sun nuna alamun COVID-19 - Sabon Bincike

Mace-macen Kano: Kashi 41 cikin 100 sun nuna alamun COVID-19 - Sabon Bincike

Bincike a kan mace-macen da ke faruwa a jihar Kano ya nuna cewa maza ne suka kwashe kashi 91 na cikin mamatan.

Rahoton binciken da jaridar The Cable ta samu ya bayyana cewa kashi 41.3 na mamatan sun rasu ne sakamakon zazzabi - daya daga cikin manyan alamomin COVID-19.

A cikin makonnin da suka gabata, an samu mace-mace a jihar wanda ya lashe rayukan manyan fitattun jama'a a Kano, jihar ta biyu a yawan jama'a a Najeriya.

A ranar Lahadin da ta gabata ne gwamnatin jihar ta amince da cewa ana samun mace-mace masu matukar bada mamaki a jihar. Amma sai ta danganta hakan da cutar zazzabin cizon sauro da sauran cututtuka da ke addabar jama'a.

Rahotanni a kan gurbacewar dakin gwajin cutar na jihar ya kara assasa hasashen cewa annobar Coronavirus ce ke kashe mutane.

Mace-macen Kano: Kashi 41 cikin 100 sun nuna alamun COVID-19 - Sabon Bincike

Mace-macen Kano: Kashi 41 cikin 100 sun nuna alamun COVID-19 - Sabon Bincike
Source: Twitter

Muhammad Garba, kwamishinan lafiya na jihar ya bayyana cewa an fara bincikar sanadin mace-macen ta hanyar jin ta bakin jama'ar da ke da dangantaka ko makwabtaka da mamatan.

Kungiyar kiwon lafiya ta duniya ta amince da wannan salon binciken amma akwai sharuddan da ake kiyayewa wajen aiwatarwa.

Tun bayan fara samun mace-macen masu matukar mamaki a jihar, Yusuf Yau Gambo, malami a fannin lissafi a jami'ar Yusuf Maitama Sule da ke Kano ya fara bincike.

Gambo ya ce rahoton ya matukar jawo hankalin kwamitin yakar cutar coronavirus ta jihar, kuma hakan zai kawo taimakon gaggawa wajen shawo kan matsalar da bayanan bogi da ke yawo.

An yi binciken ne inda aka diba gidaje 260 a fadin kananan hukumomi 17 na jihar.

Binciken kuwa ya nuna cewa gidaje 130 sun fuskanci wannan rashin da ya faru a cikin makonni biyun da suka gabata.

Kashi 67 na wadanda suka amsa tambayoyin sun ce an fara mace-macen ne daga ranar 13 ga watan Afirilun 2020.

Rahoton ya bayyana cewa an samu yawan mace-macen ne a tsakiyar birnin Kano da kuma kananan hukumomin Gwale da Dala.

Rahoton ya nuna cewa kashi 22 na wadanda suka rasun sun fara ne da zazzabi mai zafi wanda ya kaisu zuwa kwanciya a asibiti. Kashi daya bisa uku daga cikinsu kuwa sun kwashe kwanaki uku ne kafin su ce ga garinku.

Daga mahangar masana kiwon lafiya, Auwal Abubakar wanda likitan ne da ke aiki da jihar Bauchi ya alakanta mace-macen da cutar coronavirus.

"Duk da akwai matukar wahala a iya cewa ga sanadiyyar mutuwar, amma babu yuwuwar cire coronavirus daga cutukan da ake zargin ya kashesu," Abubakar yace.

"Za mu ce haka ne duba da shekarun mamatan, alamomin da suka nuna da kuma barkewar cutar a jihar," ya kara da cewa.

Kashi daya tak daga yawan mace-macen ne ake samun yara, yayin da kashi 50 daga ciki aka samu manyan magidanta masu shekaru sama da 60.

KU KARANTA KUMA: Almajirai 16 daga Kano ne suka sa yawan masu coronavirus a Kaduna ya karu - Gwamnati

A halin yanzu akwai mutum 115 da aka tabbatar suna dauke da cutar Covid-19 a jihar Kano kuma shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada umarnin rufe jihar na makonni biyu a jawabinsa na karshe ga 'yan Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel