Gwamnatin Nasarawa ta maida wasu mutane 9 da su ka dawo daga Jihar Kano
Saboda tsoron yada cutar COVID-19, an hana wasu Bayin Allah su tara da su ka fito daga Kano shiga Nasarawa. Jaridar Daily Trust ta ce an tare matafiyan ne a karamar hukumar Keffi.
Shugaban karamar hukumar Keffi, Alhaji Abdulrahman Sani-Maigoro ya maida mutanen nan da su ka kamo hanya daga Kano inda su ka fito bayan ya hana su shiga garin Keffi a ranar Talata.
Abdulrahman Sani-Maigoro ya bayyana cewa ya dauki wannan mataki ne domin kare karamar hukumarsa daga annobar Coronavirus, ya ce wannan ya na cikin umarnin da gwamnati ta bada.
Sani-Maigoro ya zanta da manema labarai a ranar Laraba a garin na Keffi ya kuma shaida masu abin da ya faru. Ya ce sun kuma tare wasu motoci cike da mutane daga Kano da jihar Legas.
Alhaji Sani-Maigoro ya ce sun umarci wadannan fasinjoji su koma garuruwan da su ka fito. Shugaban karamar hukumar ya ce ta haka ne za a hana yaduwar COVID-19 a fadin Najeriya.
KU KARANTA: Ganduje ya yi magana a game da batun sassauta dokar hana fita a Kano
Da ya ke bayani, Sani-Maigoro ya yi kira ga mutane su yi watsi da rahotannin da ke yawo na cewa ana samun wasu ‘yan kasuwan da ke shiga cikin garin Keffi daga jihar Kano cikin duhun dare.
Shugaban karamar hukumar ta Keffi a jihar Nasarawa ya ce: “Wasu bata-gari wadanda ba su neman wannan karamar hukuma da jihar mu da alheri ne su ke yada wannan mugun labari.”
Maigoro ya nuna cewa babu gaskiya a wannan labari da ake ta yadawa a kafafen sadarwa na zamani. A jawabinsa, ya yi kira ga wadannan mutane su hada-kai wajen yaki da Coronavirus.
“Na yi bakin kokarina kuma zan cigaba da yin duk abin da zan iya domin na kafa kwamitin yaki da annobar COVID-19 wanda su ke lura da tituna da duk wasu iyakokin da ke garin Keffi.”
“Na kafa kwamiti da ke aiki dare da rana domin su tabbatar mutane sun bi matakan gwamnati na yaki da COVID-19. Tare fasinjoji a motar Sharon daga Kano ya tabbatar da ana wannan aiki.”
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng