Almajirai 16 daga Kano ne suka sa yawan masu coronavirus a Kaduna ya karu - Gwamnati
- Gwamnatin jahar Kaduna ta bayyana dalilin da ya sa aka samu karuwar masu cutar coronavirus a birnin
- Ta bayyana cewa sun samu karin masu cutar ne sakamakon samun almajirai 16 da aka dawo da su jahar daga Kano dauke da cutar
- Kwamishinar lafiya ta jahar ta hankalin jami'an tsaro da su ci gaba da sanya idanu sosai a kan duk masu shiga birnin ta barauniyar hanya
Gwamnatin jahar Kaduna ta tabbatar da samun karin sabbin mutane 16 da ke dauke da cutar coronavirus a jahar.
Kwamishinar lafiya ta jahar, Dr Amina Mohammed-Baloni, ta sanar da hakan a cikin wani jawabi a ranar Alhamis, 30 ga watan Afrilu.
Ta yi bayanin cewa sabbin mutanen da aka samu da cutar sun kasance Almajirai da aka dawo da su jahar daga Kano, cewa an samu 16 daga cikinsu da cutar bayan an tura samfurin mutane 40.
Hakan na zuwa ne yan sa’o’i bayan hukumar da ke kula da hana yaduwar cututtuka ta Najeriya (NCDC) ta sanar da samun sabbin mutane 196 masu cutar a fadin kasar.
A bisa ga wani rubutu da ma’aikatar lafiyar ta wallafa a shafinta na Twitter, Kaduna ta tabbatar da sabbin mutane 17 da ke dauke da cutar kuma gaba daya alkaluman masu cutar a Najeriya ya tashi zuwa 1,728.
Boloni ta fayyace cewa daya daga cikin mutane 17 da hukumar kula da hana yaduwar cututtuka ta sanar, ya kasance maimaicin gwajin da aka yi wa wani mai COVID-19 ne sannan cewa a sanar da hukumar game da batun.
Ta kuma kara da cewa a yanzu ta tabbatar da cewar shige da ficen da ake yi wa jahar tata ce ke haddasa karuwar masu cutar a Kaduna.
Daga karshe ta kuma ta ja hankalin jami'an tsaro da su ci gaba da sanya idanu sosai a kan duk masu shiga birnin ta barauniyar hanya.
KU KARANTA KUMA: Ba za mu iya wallafa sunayen wadanda suka ci moriyar tallafin COVID-19 ba – Ministar Buhari
Ko a makon da ya gabata ma sai da gwamnatin jahar ta sanar da cewa sun samu biyar daga cikin almajiran da aka mayar wa jahar daga Kano dauke da cutar ta COVID-19.
Gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje na Kano dai ta fito da wani shiri na mayar da almajirai jihohinsu, a kokarin hana yaduwar cutar coronavirus a jahar.
Da dama masana harkar lafiya sun soki shirin bisa dogaro da cewa hakan ka iya fantsama cutar a wasu jihohin da ba su da ita.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng