An yi wa Gwamna Matawalle wankin babban bargo kan siya wa kwamishinoni manyan motocin alfarma

An yi wa Gwamna Matawalle wankin babban bargo kan siya wa kwamishinoni manyan motocin alfarma

Gwamna Bello Matawalle na jahar Zamfara na shan suka a kan siya wa kwamishinoninsa manyan motocin alfarma da ya yi, duk da matsalolin da ake ciki a kasar na annobar coronavirus.

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jahar ta soki gwamnatin jahar, inda ta bayyana siyan motocin a matsayin mara muhimmanci.

A ranar Juma’a ne Matawalle ya rarraba wa kwamishinoni 19 a jahar motoci, darakta janar na labarai da wayar da kan jama’a a jahar, Yusuf Idris ne ya bayyana hakan, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

An yi wa Gwamna Matawalle wankin babban bargo kan siya wa kwamishinoni manyan motocin alfarma

An yi wa Gwamna Matawalle wankin babban bargo kan siya wa kwamishinoni manyan motocin alfarma
Source: Twitter

Koda dai bai bayyana ainahin tsadar motocin ba, Yusuf ya bayyana cewa wadanda aka ba yan majalisar zartarwar ya yi shige da wadanda aka rarraba wa yan majalisar dokoki na jahar.

Sai dai kuma, mataimakin shugaban APC a jahar, Alhaji Sani Swamna Mayanchi, ya soki kashe kudin, cewa kamata ya yi ayi amfani da kudin wajen magance wasu matsalolin da jahar ke fuskanta.

Ya ce a kwanan nan ne annobar coronavirus ta shiga jahar. Cewa maimakon amfani da kudin wajen siyan manyan motoci da an yi amfani da shi wajen rage wa al’umma mawuyacin halin da suke ciki.

Ya kara da cewar lokaci ya yi da gwamnati za ta raba wa al’umman jahar tallafi domin rage masu radadin halin da annobar ta jefa su ciki.

Jam’iyyar ta yi zargin cewa farashin motocin guda 19 ya kai naira miliyan 570.

KU KARANTA KUMA: Budaddiyar wasikar Kwankwaso: Fadar shugaban kasa ta yi martani mai zafi

Da yake martani kan lamarin, daraktan labaran gwamnatin jahar ya ce an dade da siyan motocin tun kafin barkewar annobar coronavirus, sannan cewa an ajiye su ne a gidan gwamnati.

A gefe guda, mun ji cewa annobar cutar covid-19 ta ci ran mutum na farko a jihar Jigawa, yayin da jimillar ma su dauke da kwayar cutar a jihar ya kai mutane tara.

Kwamishinan lafiya a Jigawa, Dakta Abba Zakari, ne ya sanar da hakan yayin gabatar da jawabi ga manema labarai a matsayinsa na shugaban kwamitin kar ta kwana na jiha a kan annobar covid-19.

Da ya ke sanar da hakan a Dutse, babban birnin jihar Jigawa, kwamishinan ya ce an kara rufe wasu kananan hukumomi hudu; Dutse, Gwaram, Miga da Auyo.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel