Shahararren jarumin fina-finan Indiya Irrfan Khan ya rasu

Shahararren jarumin fina-finan Indiya Irrfan Khan ya rasu

- Shahararren jarumin fina-finan Indiya Irrfan Khan ya rasu a ranar Laraba bayan ya yi fama da cutar kansan hanji

- Jarumin ya taka gagarumin rawar gani a fina-finan Hollywood kamar su Jurrasic Park da fina-finan Turai

- Khan ya rasu ya bar matar aure daya da yara biyu, Babil da Ayan

Fitaccen jarumin fina-finan Indiya, Irrfan Khan, wanda ya taka rawar gani har a fina-finan Hollywood ya rasu yana da shekara 53 bayan ya yi fama da ciwon kansan hanji.

Khan ya rasu ne a wani asibiti mai suna Kokilaben Dhirubhai Ambani da ke birnin Mumbai a ranar Laraba, 29 ga watan Afrilu.’

A cewar jaridar Indian Times, jarumin ya sha fama da cutar kansa tun a shekarar 2018 sannan kakakinsa ya tabbatar da cewar yana ta samun kulawar likitoci.

A yan kwanaki da suka gabata kakakin nasa ya fitar da wata sanarwa inda ya bukaci masoyansa da kada su tayar da hankali, sannan ya yi masu alkawarin cewa zai dunga sanar dasu bayanai game da halin da ake ciki.

An tattaro cewa a 2018, Khan ya fadi kalaman “Na yi imani, na mika wuya,” a cikin wani jawabi da ya ke magana game da fama da yake yi da cutar kansa.

Fim din karshe da jarumin ya yi shine Angrezi Medium, wanda ake haskawa yan kwanaki kafin a sanar da dokar kulle a kasar Indiya. Hakan ya sanya an dakatar da haska fim din a wuraren kallo saboda haramci da aka sanya a taron jama’a.

KU KARANTA KUMA: COVID-19: Mahaifiyata ta umurce ni da na aske gemuna bayan na warke – El-Rufai

Marigayin ya rasu ya bar matar aure daya da yara biyu, Babil da Ayan.

A wani labari na daban, mun ji cewa gwamnan jahar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana mutuwar wasu mutane 3 daga cikin mutane 10 dake dauke da cutar Coronavirus a jahar.

Jaridar Punch ta ruwaito gwamnan ya bayyana haka da tsakar daren Talata, 28 ga watan Afrilu, ta bakin hadiminsa a kan harkokin watsa labaru, Muhammad Bello.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng