Babu ranar bude makarantu tukuna duk da an sassauta takunkumi – Ministan ilmi

Babu ranar bude makarantu tukuna duk da an sassauta takunkumi – Ministan ilmi

Tun a karshen watan Maris gwamnatin tarayya ta rufe duk wasu makarantu a Najeriya. Har yanzu ba a bada iznin bude makarantun ba, kuma gwamnati ta ce babu ranar hakan har gobe.

Karamin ministan ilmi, Emeka Nwajiuba, ya yi magana game da lokacin da ‘yan makaranta za su koma bakin karatu. Ministan ya ce ba ya iya hangen ranar da za a bude ajin karatu a nan kusa.

Hon. Emeka Nwajiuba ya yi wannan jawabi ne a lokacin da ya ke amsa tambayoyi yayin da kwamitin shugaban kasa da ke yaki da annobar cutar COVID-19 ta kira taron ‘yan jarida a Abuja.

Nwajiuba ya ke cewa duk da gwamnatin tarayya ta sassauta takunkumin kulle, babu batun bude makarantu tukuna. Kwamitin na shugaban kasa ya zanta da manema labarai ne ranar Talata.

Karamin ministan ilmin na Najeriya ya ce: “Shugaban kasa ya fara tabo batun bude tattalin arziki sannu a hankali. Idan har ba ayi wannan ba, ba na ganin lokacin da za a sake bude makarantu.”

KU KARANTA: INEC ta ce ba ta canza matsaya kan zabukan gwamnonin da za ayi a bana ba

Babu ranar bude makarantu tukuna duk da an sassauta takunkumi – Ministan ilmi

Karamin Ministan ilmi ya ce babu maganar bude makarantu a yanzu
Source: Twitter

Emeka Nwajiuba ya ce muddin shugaban kasa Buhari bai fara maganar jama’a su koma wuraren aikinsu ba, ba zai iya cewa ga ainihin lokacin da za a bude makarantun da ke fadin kasar ba.

“Ba zai yi mana daidai mu saka maku rana ba. Dole sai an bi matakai kafin a bude makarantu. Ba za mu so mu jefa yaranmu a hadari ba. Makarantun ba za su iya aiki ba tare da al’umma ba.”

Game da yadda ‘yan makaranta za su motsa zuwa aji na gaba, ministan ya ce: “Za ayi jarrabawa lokacin da mu ka gamsu cewa yara sun koyi abin da su ke bukata su tafi zuwa aji na gaba”

“Ga wadanda su ke shirin kammala karatun karama ko babbar sakandare, mu na kintsasu, kuma za mu cigaba da yi masu tanadi. Za mu yi kokarin ganin sun shiryawa manyan jarrabawa.”

“WAEC ba ta fasa jarrabawar karshen shekara ba, an dakatar da jarrabawan ne zuwa wani lokaci. ‘Dalibanmu za su je su zana jarrabawar nan gaba idan mun shiryasu.” Inji Ministan kasar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel