Annobar covid-19 ta harbi sabbin mutane 195 a Najeriya, 38 a Kano

Annobar covid-19 ta harbi sabbin mutane 195 a Najeriya, 38 a Kano

Hukumar yaki da cututtuka ma su yaduwa a kasa (NCDC) ta sanar da cewa karin sabbin mutane 195 ne aka tabbatar suna dauke da kwayar cutar covid-19 a fadin Najeriya.

A cikin sanarwar da NCDC ta fitar bayan 12:00 na dare a shafinta na tuwita, ta fitar da jerin jihohi da jimillar ma su dauke da kwayar cutar a kowacce jiha kamar haka;

80-Lagos

38-Kano

15-Ogun

15-Bauchi

11-Borno

10-Gombe

9-Sokoto

5-Edo

5-Jigawa

2-Zamfara

1-Rivers

1-Enugu

1-Delta

1-FCT

1-Nasarawa

NCDC ta ce ya zuwa karfe 11:50 na daren ranar Talata, 28 ga watan Afrilu, akwai jimillar mutane 1532 da aka tabbatar da cewa suna dauke da kwayar cutar covid-19 a Najeriya.

An sallami mutane 255 bayan an tabbatar da samun saukinsu, a yayin da cutar ta hallaka jimillar mutane 44.

DUBA WANNAN: Ganduje ya yi magana a kan tallafin covid-19 da Buhari ya sanar zai bawa Kano

A wani labarin da Legit.ng ta wallafa, an bayyana cewa tawagar kwarrarun ma'aikatan Lafiya 15 da suka zo Najeriya daga China domin taimakawa kasar wurin yaki da COVID-19 basa dauke da kwayar cutar.

Ministan Lafiya, Osagie Ehanire, ne ya fadi hakan yayin taron da kwamitin kar ta kwana na shugaban kasa kan yaki da COVID-19 ya gudanar ranar Talata.

Enahire ya ce sakamakon gwajin da aka yi ya nuna dukkan yan kasar na China ba su dauke da kwayar cutar.

Wannan na zuwa ne bayan sun kwashe kwanaki 14 a killace domin tabbatar da cewa ba su kamu da cutar ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng