Za a yi bincike kan mace-macen Kano - Buhari

Za a yi bincike kan mace-macen Kano - Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana damuwa dangane da yawan mace-macen da ake ci gaba da samu a jihar Kano da ke Arewacin kasar.

Buhari ya bayyana damuwarsa ne cikin jawaban da ya gabatar ga 'yan kasar kan annobar cutar korona a ranar Litinin da daddare.

Shugaban ya ce gwamnatinsa ta aika da tawagar kwararrun domin aiwatar da bincike tare da shimfida dokar kulle a jihar har na tsawon makonni biyu.

Furucin shugaban kasar ya zo ne bayan yawan mace-macen da aka samu a jihar Kano wadda ta zarce ta kowane lokaci da aka samu a baya.

A yayin da likafar annobar korona ta ke ci gaba, tuni dai mun ji cewa gwamnatin tarayya ta aika da kwamitin tawagar mutum 17 zuwa Kano domin gudanar da bincike kan lamarin a jihar.

Har ila yau dai fargaba ta mamaye zukatan al'ummar Kano da kuma kasancewa cikin hali na rashin tabbas kan musabbabin da ya haifar da mace-macen da ake samu cikin wannan lokaci da ake fama da annobar korona.

Da dama dai ana zargin cewa cutar korona ce ke yiwa mutane illa a Kanon yayin da wasu ke alakanta mace-macen da cututtuka irinsu hawan jini, sankarau, zazzabin cizon sauro, ciwon sukari da sauransu.

Babu shakka tun daga mako jiya kawo yanzu, ana ci gaba da samun yawaitar mace-macen mutane a kusan dukkanin unguwannin da ke cikin birnin Kano musamman dattawa da suka hada da manyan ma'aikatan gwamnati, malaman jami'a da sauransu.

Shugaban Najeriya; Muhammadu Buhari

Shugaban Najeriya; Muhammadu Buhari
Source: Twitter

Ganin irin yawan mace-macen da ake samu a jihar, ya sanya tsohon gwamnan jihar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya aikewa shugaba Buhari wasika, ya na rokon a kawowa jihar dauki.

A cikin wasikar da ya aikewa shugaban kasar, Sanata Kwankwaso ya bukaci gwamnatin tarayya da ta gaggauta ceton rayukan al'ummar jihar Kano.

Ko a ranar Asabar da ta gabata, fiye da mashahuran mutane 10 'yan asalin jihar Kano sun riga mu gidan gaskiya. Cikin su akwai editan babban kamfanin jaridar nan ta Triumph, Musa Tijjani.

Sauran mashahuran mutanen da ajali ya cimma a ranar Asabar din sun hadar da; Farfesa Ibrahim Ayagi, Dr. Musa Gwarzo, Dahiru Rabiu, Adamu Dala, Salisu Lado, Shamsiyya Mustapha, Nene Umma, Garba Fagge, Nasiru Bichi, Farfesa Aliyu Umar Dikko da kuma Aminu Yahaya.

Har a yau Talata mun samu cewa an yi jana'izar daya daga cikin manyan limaman masallacin Murtala na Kano, Sheikh Tijjani Bala Yola.

Wata majiya mai kusanci da marigayin ta sanar da jaridar The Cable cewa, Sheikh Yola ya yi kacibus da ajali a safiyar ranar Talata a gidansa da ke unguwar Gwale a cikin birnin Kano.

Haka kuma a wayewar garin yau, Uba Adamu, mahaifin Farfesa Abdallah Adamu, shugaban jami'ar koyo daga gida ta Najeriya NOUN, ya riga mu gidan gaskiya a birnin na Kano.

Kazalika ajali ya katse hanzarin Adamu Sarawa, tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Jigawa. Ya mutu ne a daren jiya a gidansa da ke Kano.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel