Covid-19: Mutane fiye da 100 sun mutu bayan sun sha wani jikon maganin gargajiya

Covid-19: Mutane fiye da 100 sun mutu bayan sun sha wani jikon maganin gargajiya

Mutane 109 sun mutu a jumhuriyar Dominican bayan sun sha wani jiko da sunan maganin COVID-19.

A bisa ga jaridar AS ta kasar Espanya, jikon gargajiyan ya fito ne daga yankin Haiti, wata kasa da ke makwabtaka da tsibirin Caribbean.

An tattaro cewa mutane da dama sun sha jikon wanda aka yi da rake, da sunan na hana yaduwar cutar Coronavirus.

Covid-19: Mutane fiye da 100 sun mutu bayan sun sha wani jikon maganin gargajiya
Covid-19: Mutane fiye da 100 sun mutu bayan sun sha wani jikon maganin gargajiya
Asali: UGC

Ministan lafiya na kasar, Rafael Sanchez, ya ce jimlar mutane 130 ne suka sha jikon amma mutane 109 ne kadai suka rasa rayukan su.

“Binciken likitoci ya nuna cewa mutanen guda 109 sun mutu ne sakamakon shan jikon maganin da suka yi, wanda sama da kaso 50 cikin dari giya ne,” in ji Sanchez.

Ministan ya ce yan sanda na ta kwace tarin jikon a cikin jumhuriyar Dominican a yan makonnin da suka gabata.

KU KARANTA KUMA: Dan Atiku ya warke daga coronavirus bayan kwanaki 40 a killace

Ya ce ana kokarin kama wadanda suka hada jikon da rarraba giyan wanda baya bisa ka’ida.

Ministan ya ce a lokuta da dama, ya yi watsi da labarin karyan cewa giyan na warkar da masu cutar COVID-19.

Kasar ta samu masu Coronavirus guda 5,926 sannan 273 sun rasa rayukansu sakamakon cutar.

A wani labari na daban, mun ji cewa fitaccen ‘dan siyasar Najeriya, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya yi magana game da mutuwar Lateef Raheem. Marigayin ya kasance babban dogari na-hannun daman Bola Ahmed Tinubu.

Jagoran na jam’iyyar APC mai mulki ya fitar da jawabi daga ofishinsa ne a ranar Litinin. ‘Dan siyasar ya tabbatar da cewa jami’in tsaron na sa ya mutu ne a sanadiyyar cutar Coronavirus.

Bola Tinubu ya ce: “Bayan mutuwar babban jami’in tsaronmu, Alhaji Lateef Raheem, ma’aikatan NCDC sun yi dabarar daukar jininsa domin ayi gwaji a gano ainihin cutar da ta kashe shi.”

Jawabin ya kara da cewa: “A yau (Litinin) an dawo da sakamakon gwajin da aka yi, an gano ya na dauke da kwayar cutar COVID-19. An killace wani hadimi da aka samu dauke da cutar”

“A matsayin rigakafi Bola Tinubu da mai dakinsa sanata Oluremi Tinubu da duk wasu hadimansu, sun yi gwajin kwayar cutar COVID-19 bayan mutuwar Alhaji Lateef Raheem, a ranar Asabar.”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel