Gwamnan Gombe ya maida Almajirai jihohinsu, Gwamnatin Wike za ta bi sahu

Gwamnan Gombe ya maida Almajirai jihohinsu, Gwamnatin Wike za ta bi sahu

Bayan yarjejeniyar da gwamnonin jihohin Arewa su ka cin ma a makon jiya, gwamnatin jihar Gombe ta maida almajirai 700 zuwa ainihin jihohin da su ka fito a cikin farkon makon nan.

Kwamishinan harkar ilmi na jihar Gombe, Dr. Habu Dahiru, ya shaidawa manema labarai cewa gwamnatinsu ta tattara wadannan almajirai da ke karatu a jihar, ta maida su jihohinsu.

Dr. Dahiru ya ce gwamnatin jihar Gombe ta dauki wannan mataki ne domin a samu damar kula da annobar cutar COVID-19 da yanzu ta ke cigaba da harbin Bayin Allah a fadin Duniya.

A cewar Habu Dahiru, gwamnatin Gombe ta samu goyon bayan malaman addini kafin ta dauki matakin zartar da wannan hukunci. Dahiru ya ce za a kai almajiran duk inda su ka fito.

Da ya ke magana, kwamishinan ilmin ya ke cewa gwamna Inuwa Yahya ya amince a maida wadannan almajirai 700 zuwa yankin da su ka fito a cikin jihohin Arewacin Najeriya 19.

KU KARANTA: Gwamnatin Kano ta maida Almajirai zuwa Jihohin Jigawa da Katsina

Gwamnan Gombe ya maida Almajirai jihohinsu, Gwamnatin Wike za ta bi sahu
Gwamnatin Jihar Gombe ya maida Almajirai jihohin da su ka fito
Asali: UGC

Dahiru ya ke fadawa maneman labaran cewa:"A cikin motar da aka fara zuba almajiran akwai wadanda su ka fito daga Bauchi, Borno, Sokoto, Kebbi, Katsina, Zamfara, Kano da dai sauransu."

“Za a dauki lokaci ana wannan aiki, kun lura cewa ba mu so mu zuba mutane da yawa sosai a cikin mota guda, mu na da motocin Gombe Line 65, ba haka nan kurum mu ka tura su ba...”

Kwamishinan ya kara da cewa: “...Mun rubuta wasika dauke da sunan kowane almajiri. Da zarar an isa jiharsa, za a mika shi ga wata makaranta a karkashin shirin samar da ilmi ga kowa.”

“Saboda haka mu na daukarsu sahu bayan sahu mu mika su ga gwamnatin jihohinsu, dauke da jami’an tsaro da ke yi masu rakiya.” Dr. Dahiru ya yi wannan jawabi ne a fadar sarkin Gombe.

Shi ma gwamnan Ribas, Nyesom Wike ya bada sanarwa a ranar Litinin cewa zai maida almajirai jihohin da su ka fito. Wike ya ce dole ya yi hakan domin kare lafiyar mutanen jihar Ribas.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel