JAMB: Gine-gine da Makarantun Farfesa Ojerinde sun koma hannun hukuma - Kotu

JAMB: Gine-gine da Makarantun Farfesa Ojerinde sun koma hannun hukuma - Kotu

A wata sanarwa da aka fitar a jaridun gida, gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ta karbe wasu kadarori na tsohon shugaban hukumar jarrabawa ta JAMB a sakamakon bincike da ake yi.

Sanarwar ta tabbatar da cewa gwamnati ta karbe tulin dukiyar da tsohon shugaban JAMB, Farfesa Dibu Ojerinde ya mallaka ne ta hannun hukumar ICPC mai binciken barayi a kasar.

“Hukumar ta na binciken Dibu Ojerinde na jami’ar Obafemi Awolowo da ke Ile-Ife a jihar Osun, a game da wasu kadarori da ake cewa Dibu Ojerinde ya mallaka.” Sanarwar ta bayyana.

Jawabin da ICPC ta fitar, ya ce: “Hukumar ta na da ra’ayin cewa, a binciken da ta gudanar, kadarorin Ojerinde sun yi yawa, idan aka yi la’akari da albashinsa da kuma wasu abubuwa.”

A dalilin haka ICPC mai yaki da barayi ta karbe kadarorin wannan malamin wanda ya taba rike shugaban hukumar JAMB mai gudanar da jarrabawar shiga makarantun gaba da sakandare.

ICPC ta ce wadannan karafaren gidaje da gidajen mai da kuma makarantu da aka karbe su na dauke ne da sunan Dibu Ojerinde ko lauyoyinsa ko kuma wasu da su ke fakewa da sunansa.

KU KARANTA: Wani Gwamnan PDP ya sake maidawa Buhari tallafin da ya ba jiharsa

1. Makarantar Trillion Learning Centre da ke Ilorin, jihar Kwara

2. Gidan ma MRS da ke titin Sango Road a Ilorin, jihar Kwara

3. Gidan rawan Sound Bar Club House da ke GRA, Ilorin, jihar Kwara

4. Makarantar Kiddies Cove Educare da ke GRA, Ilorin, jihar Kwara

5. Kamfanin Cheng Marble da ke Ganmo, Ilorin, jihar Kwara

6. Katafaren gida mai dakuna 5 mai lamba na 42 EFAB a Abuja.

7. Katafaren gida mai dakuna 4 mai lamba na 7 EFAB a Abuja.

8. Gida mai dakuna 2 mai lamba na 9, EFAB a Abuja.

9. Gida mai dakuna 3 mai lamba na 4 a Kadu, a Abuja.

10. Gidan man Parkan filling station a Ibadan jihar Oyo.

11. Dakin kwana na Oke-Afin Hostel da ke kusa da jami’ar fasahar Ladoke Akintola a garin Ogbomosho, jihar Oyo

12. Wani gida mai dakuna 3 mai lamba na 4 a yankin Achimota a birnin Accra da ke kasar Ghana.

Jaridar Premium Times ta ce kotu ta bada damar soma rike kadarorin. Ana zargin cewa Ojerinde ya mallaki gidan ne da wasu kudi da ya wawura tsakanin 2016 zuwa 2017 a hukumar JAMB.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel