Uba da Da sun shiga hannu bayan sun kashe dan Fulani makiyayi a jahar Ogun
Wani magidanci dan shekara 45, Kolese Womiloju tare da dan sa dan shekara 25, Taiwo sun fada hannun hukuma bayan an same su da laifin kashe wani matashin dan Fulani makiyayi.
Jami’an rundunar Yansandan Najeriya reshen jahar Ogun ne suka samu nasarar kama Uba da Dan, inda suke zarginsu da kashe wani bahillace, Abubakar Usman dan shekara 32.
KU KARANTA: Ruwan sama kamar da bakin kwarya ya lalata gidaje 271 a jahar Kaduna
Jaridar Punch ta ruwaito Uba da Dan sun kashe Abubakar ne saboda ya kyale shanunsa sun shigar musu gona a kauyen Gbagba Elewure dake cikin karamar hukumar Odede na jahar Ogun.
Jami’i mai magana da yawun rundunar Yansandan jahar, Abimbola Oyeyemi ne ya bayyana haka yayin da yake ganawa da manema labaru a ranar Lahadi, 26 ga watan Afrilu.
“Mun kama su ne a ranar Laraba bayan samun rahoton aikata laifin kisan, yayan mamacin, Bello Usman ne ya kai kara ofishin Yansanda dake Odeda game da bacewar kaninsa. Bello ya shaida ma Yansanda cewa dan uwansa na da garken shanu a Gbagba, amma basu gan shi ba.
“Jin hakan ke da wuya Yansanda suka bazama nemansa, zuwa yamma aka gano gawarsa a cikin wani rijiya dake cikin dajin, inda aka jefa shi bayan an kashe shi, Yansandan sun ga saran adda sosai a duk jikinsa.
“Bayan sun tabbatar cewa kashe mamacin aka yi, sai DPO na Yansandan yankin CSP Ajayi Williams ya fara binciken sirri, a haka suka kama Uba da Dan, bayan sun sha tambayoyi sun amsa laifinsu, inda suka ce sun kashe shi ne saboda sun hangi shanunsa a cikin gonarsu.
“A cewarsu sun gargde shi ya dauke shanunsa daga gonar, amma ya ki, ganin haka suka buge shi da zoben tsafi, daga nan ya fita hayyacinsa, daga nan ne suka dinga sararsa har sai da ya mutu, sa’annan suka ja gawar a kasa tafiyar kilomita 1 zuwa tsohuwar rijiyar da suka jefa shi a ciki.” Inji shi.
Kakaakin yace kwamshinan Yansandan jahar, Kenneth Ebrimson ya bada umarnin mika binciken lamarin ga sashin binciken manyan laifuka na rundunar Yansandan jahar
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng