Duk abin da na mallaka a Duniya gumina ne ba kwangilar gwamnati ba - Melaye

Duk abin da na mallaka a Duniya gumina ne ba kwangilar gwamnati ba - Melaye

Fitaccen ‘dan siyasar Kogi Dino Melaye ya yi wata hira ta fiye da rabin sa’a a shafin Instagram. Dele Momodu shi ne wanda ya shirya wannan hira kai-tsaye da tsohon ‘dan majalisar.

A hirar da aka yi da ‘dan siyasar, ya yi magana game da dukiyarsa da ake yawon magana a kai. Sanata Dino Melaya ya fayyacewa jama’a cewa gumi ya yi wajen mallakar arzikin na sa.

Dino Melaye ya bayyana cewa zagewa ya yi ya samu dukiya ba wai ta karkashin gwamnati ya bi ba. Melaye ya ce bai taba yi wa gwamnati wata kwangila da har ta sa ya samu kudi ba.

Melaye ya bayyana wannan ne a lokacin da mai gidan jaridar nan ta Ovation watau Dele Momodu ya tambaye sa ko ya na da wani abu da ya ke boyewa ganin yadda ake yawon bincikensa.

Sanata Melaye ya ce sau da-dama an saba turo jami’an hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon-kasa domin su yi bincike a game da dukiyar da ya mallaka.

KU KARANTA: Dino Melaye ya fadawa Mabiyansa maganin cutar Coronavirus

Melaye ya taba rike kujerar majalisar wakilan tarayya. A shekarar 2015 kuma ya zama sanatan Kogi ta yamma a majalisar dattawa a APC. Bayan shekaru uku, ya sauya-sheka zuwa PDP.

A wannan hira, tsohon ‘dan majalisar tarayyar Najeriyar ya ce abin da EFCC ba ta bincika a game da shi ba, shi ne kawai cibiyar haihuwarsa wanda mahaifiyarsa kadai ta san inda ta bizne.

Wannan doguwar hira da Momodu ya yi da Sanata Melaye ta dauki kusan mintuna 37 a dandalin Instagram. Melaye ya yi bayani game da irin kokarin da ya yi a lokacin da ya ke majalisa.

Sanatan ya ce ya taba kawo wani kudiri a majalisar wakilai da dattawa da nufin gyara asibitocin Najeriya, a cewarsa da an amince da kudirin da yanzu an iya cin karfin annobar COVID-19.

Kawo yanzu tsohon ‘dan majalisar ya kalubalanci sauran ‘yan siyasa su fito su fadi silar arzkinsu. Kawo yanzu Melaye ya na ta taimakawa mutanen Kogi da agaji a lokacin wannan annoba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Online view pixel