An fara barin mutanen Saudiyya su je kasuwa face a Garin Makka
Bayan tsawon lokaci da maka takunkumin zirga-zirga a jihohin Saudi Arabiya, mahukuntar kasar sun sassauta wannan takunkumi domin a rike bude wuraren cefanen azumi.
Rahotanni daga gidan yadan labarai na Saudi Arabiya sun bayyana cewa gwamnati ta cire takunkumin sa’a 24 da ta garkama a baya, yanzu mutane za su samu damar fita.
Hukuma ta bada iznin a rika bude kasuwanni da shaguna daga karfe 9:00 na safe zuwa karfe 5:00 na yamma. Hakan na nufin an ba mutane tsawon sa’a takwas domin su yi cefane.
Jawabin da gwamnatin kasar ta fitar ya nuna cewa wannan doka za ta yi aiki a fadin kasar illa irinsu birnin Makkah. Har yanzu a yankin Makka kowa zai cigaba da zama a gida.
A garin Makkah wannan cuta ta COVID-19 ta yi kamari. Kawo yanzu fiye da mutum 130 su ka mutu a kasar a sakamakon Coronavirus. Akwai mutane 16, 000 da ke dauke da cutar.
KU KARANTA: Najeriya ta samu karin mutane 87 da ke dauke da cutar COVID-19
A watan da ya gabata ne gwamnatin Saudi ta sanar da cewa babu ibadar hajji a wannan shekarar. Saudi Arabiya ce kasar da wannan annoba na COVID-19 ya fi tabawa a yankin Larabawa.
A shekarar bara, an samu sama da mutane miliyan biyu da rabi da su ka halarci aikin hajji. Musulman Duniya su kan ziyarci wannan kasa a irin wannan lokaci domin sauke farali.
Ta’adin wannan annoba dai ya sa gwamnatin Saudi ta rufe duk wasu wuraren kallon wasanni da dakunan cin abinci. Haka zalika yanzu ba a barin jirage su tashi ko su shigo wannan kasa.
Sarkin Saudi, Muhammad Bn Salman Al Saud da ya ke bada wannan sanarwa, ya ce dokar za ta fara aiki ne daga ranar laraba 29 ga watan Afrilu zuwa ranar 13 ga watan Mayun gobe.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng