Abba Kyari: Babu ruwan APC a wanda zai zama shugaban ma’aikatan Shugaban kasa na gaba - Issa-Onilu

Abba Kyari: Babu ruwan APC a wanda zai zama shugaban ma’aikatan Shugaban kasa na gaba - Issa-Onilu

- Jam’iyyar APC ta ce ba za ta sanya baki a wajen zabar wanda zai zama shugaban ma’aikatan shugaban kasa Muhammadu Buhari na gaba ba, bayan rasuwa Abba Kyari

- Lanre Issa-Onilu, kakakin APC, ya ce hakkin shugaban kasa ne ya nada wanda ya ke so a matsayin

- Ana ta hasashen wadanda za su gaji Kyari ciki harda Babagana Kingibe, wanda ya kasance babban dan siyasa

Ana tsaka da kace-nace kan wanda zai zama shugaban ma’aikatan shugaban kasa na gaba, jam’iyyar All Progressives Congress (APC), ta ce ba ta damu da wanda zai maye gurbin Abba Kyari ba.

Jam’iyyar mai mulki, a wata sanarwa daga kakakinta Malam Lanre Issa-Onilu, ta ce nadin shugaban ma’aikatan shugaban kasa na a karkashin ikon shugaban kasa Muhammadu Buhari ne, jaridar The Nation ta ruwaito.

Legit.ng ta lura cewa tun bayan mutuwar Abba Kyari, wanda ya rasu sakamakon cutar COVID-19, manyan yan Najeriya da dama na ta kokarin ganin sun maye gurbinsa.

Babagana Kingibe, wanda ya kasance babban dan siyasa ne kan gaba a tseren.

Abba Kyari: Babu ruwan APC a wanda zai zama shugaban ma’aikatan Shugaban kasa na gaba - Issa-Onilu
Abba Kyari: Babu ruwan APC a wanda zai zama shugaban ma’aikatan Shugaban kasa na gaba - Issa-Onilu
Asali: UGC

Da yake martani kan hasashen cewa APC na iya taka rawar gani wajen zabar shugaban ma’aikatan na gaba, kakakin jam’iyyar mai mulki ya ce jam’iyyar ba za ta sanya baki a lamarin ba.

KU KARANTA KUMA: An kama mai cutar coronavirus da ya tsere a jahar Borno

Ya yi gargadi a kan siyasantar da matsayin yayinda ya ke jadadda cewa shugaban kasar ne ke da ikon zabar duk wanda ya ke so.

Kan hasashen cewa wasu manyan yan siyasa na iya taka rawar gani, kakakin na APC ya ce: “Mutane na ta kidinsu da rawarsu ne. Ta yaya wani mutum ko jam’iyya za su zabi wanda zai ‘dare matsayin?

A wani labarin kuma, mun ji cewa gamayyar wasu kungiyoyin goyon bayan shugaban kasa, Muhammadu Buhari, sun yi kira gare shi da ya nada Injiniya Kilani Mohammed a gurbin marigayi Abba Kyari, tsohon shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa.

Gamayyar kungiyoyin a karkashin inuwar PBS sun bayyana cewa akwai bukatar Buhari ya samu gogaggen dan siyasa da ya san aiki domin nada shi a gurbin da marigayi Kyari ya bari.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel