Emma Theofilus: ‘Yar autar Ministoci a Gwamnatin tarayyar kasashen Afrika

Emma Theofilus: ‘Yar autar Ministoci a Gwamnatin tarayyar kasashen Afrika

A kasar Nambiya, an ga abin da ba a saba gani a Nahiyar Afrika ba, inda wata Budurwa ta zama ministan gwamnatin tarayya. Jaridar Face 2 Face Afrika ta fitar da wannan rahoto.

Emma Theofilus mai shekaru 23 a Duniya ta samu kujerar ministar yada labarai da fasaha a gwamnatin kasar Namibiya. Wannan ya sa Emma Theofilus ta shiga littafin tarihi.

Wannan nadi da aka yi wa budurwar ya jawo ce-ce-ku-ce daga mutane. Ko da cewa Miss Theofilus za ta rike kujerar karamar minista ne, wasu su na ganin ba ta cancanta ba.

Da wannan nadi da aka yi, Emma Theofilus ta zama ‘yar autar ministocin kasar Nambiya, haka zalika ita ce wanda ta fi kowa karancin shekaru a majalisar gwamnatin kasar Afrikar.

Wannan Baiwar Allah ta maidawa masu sukar nadin mukamin da aka yi mata martani, inda ta yi watsi da surutan da jama’a su ke yi na cewa ba ta san kan aiki a ‘yan shekarun ta ba.

KU KARANTA: Wani fitaccen Farfesan tattalin arziki a Najeriya ya mutu

“Ba na tunanin ni wata daban ce da sauran jama’a, haka kuma ba na ganin cewa ban san aiki ba, haka zalika ba na tunanin mukamin da aka ba ni ya na da alaka da zama na mace ko mai karancin shekaru.” Sabuwar ministar ta ke cewa babu wani aikin da zai gagare ta.

“Don haka maganar ace ban san kan aiki ba, ba ta taso ba.” Theofilus ta kara da cewa: “Ina cike da farin ciki. An fada mani cewa ni zan zama mizanin awon matasa a cikin gwamnati”

A wata hirar da aka yi da ministar, ta ce: “Na karbi wannan kalubale kamar yadda na dauki sauran mukamai.” Theofilus ta ce ta san wahalar irin wannan aiki na sha'anin siyasa.

Kafin yanzu Miss Theofilus jami’ar shari’a ce a ma’aikatar shari’a ta gwamnatin Namibiya. A ma’aikatar, ta yi kokari wajen kawo gyara kan keta hakkin mutanen kasar da ake yi.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel