Yanzu Yanzu: Jami’in WHO na uku da wasu mutane 2 sun kamu da COVID-19 a Bauchi

Yanzu Yanzu: Jami’in WHO na uku da wasu mutane 2 sun kamu da COVID-19 a Bauchi

Wani jami’in hukumar lafiya ta duniya da wasu mutane biyu sun kamu da cutar Coronavirus a jahar Bauchi.

A yanzu jumular mutane shida kenan ke da cutar ta COVID-19 a jahar, wanda uku daga cikinsu suka kasance jami’an hukumar WHO.

Wani jami’in WHO ya fara kamuwa da COVID-19 a ranar Lahadi, yayinda aka tabbatar da kamuwar mutum na biyu a ranar Talata.

Yanzu Yanzu: Jami’in WHO na uku da wasu mutane 2 sun kamu da COVID-19 a Bauchi

Yanzu Yanzu: Jami’in WHO na uku da wasu mutane 2 sun kamu da COVID-19 a Bauchi
Source: Twitter

A cewar jami’in labaran cibiyar lafiya ta jahar Bauchi, Ibrahim Sani, an karbi sakamakon gwajin ne daga cibiyar kula da yaki da cututtuka na Najeriya a daren ranar Alhamis.

Sani ya ce sauran mutane biyun da suka kamu sun kasance wadanda suka dawo daga jahar Lagas.

“Gaskiya ne cewa Bauchi ta samu sabbin mutane uku da suka kamu. Kamar yadda ku ka sani zuwa yanzu, an sallami marasa lafiya biyar bayan sun warke.

“Da sabbin mutanen nan da suka kamu, a yanzu haka akwai mutane shida kenan da ke da cutar a jahar. Sannan babu wanda ya mutu."

KU KARANTA KUMA: Jihohi 27 da aka samu bullar cutar Covid-19 a Najeriya - NCDC

A wani labarin kuma, mun ji cewa Gwamnan jahar Bauchi, Bala Muhammad ya sanar da umarnin garkame wuraren bauta, wuraren taron jama’a da kuma kasuwanni a kokarinsa na dakile yaduwar cutar Coronavirus.

Daily Trust ta ruwaito gwamnan ya bayyana haka ne yayin da yake ma al’ummar jahar jawabi a ranar Alhamis, inda yace ya dauki matakin ne bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki.

Gwamnan yace sun tattauna matsalar yaduwar cutar a Bauchi, da sauran matsalolin kiwon lafiya da suka dabaibaye al’ummar jahar.

A yanzu akwai mutane 8 dake dauke da cutar a jahar.

Gwamnan ya kara da cewa sun dakatar da duk wani gangamin sauraron tafsirin Al-Qur’ani a watan azumin Ramadana, sai dai ga mai karatu da mai fassara kadai.

Gwamnan ya ja kunnen Musulmai da cewa kada su ga don an shiga watan Ramadan su yi sakaci da dokar kare yaduwar annobar, don haka yace ya dakatar da asham, tahajjud da I’itikaf.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel