Ka da a kara wa’adin zaman kulle – kungiyar NLC ga Gwamnatin tarayya

Ka da a kara wa’adin zaman kulle – kungiyar NLC ga Gwamnatin tarayya

Kungiyar kwadago ta yi kira ga gwamnatin tarayya da cewa ka da a kara wa’adin zaman kullen da ake yi. Gwamnati ta dauki wannan mataki ne domin takaita yaduwar cutar COVID-19.

Shugaban kungiyar kwadagon Najeriya ta NLC, Ayuba Wabba ya rubuta wata takarda ga shugaban kwamitin da shugaban kasa ya kafa domin yaki da annobar COVID-19 a Najeriya.

Kwamred Wabba ya fadawa wannan kwamiti cewa jama’a za su tagayyara a babban birnin tarayya da sauran jihohin da aka maka masu wannan takunkumi makonnin da su ka wuce.

A wannan wasika da shugaban ‘yan kwadagon ya rubuta a ranar 14 ga watan Afrilu, 2020, NLC ta nuna rashin jituwarta game da tsarin da gwamnatin tarayya ta ke bi wajen kaya bada tallafi.

“Yayin da mu ka fahimci amfanin kara wa’adin takunkumi ta fuskar kiwon lafiya, ya kamata ayi la’akari da cewa wuraren da aka sa takunkumi su ne kirjin kasuwancin kasar.” Inji NLC.

KU KARANTA: Nan gaba ba za a samu kudin da za a rabawa Jihohi ba - NGF

Ka da a kara wa’adin zaman kulle – kungiyar NLC ga Gwamnatin tarayya

Shugaban NLC ya nemi Gwamnatin tarayya ta fara shirin sassauta takunkumi
Source: UGC

“Hakan abu ne mai hadari, duk yadda ya ke da amfani a hana jama’a mutuwa daga cutar Coronavirus, rashin abin yi a dalilin wannan zai iya jawo wasu cututtuka har da mutuwa.”

Wabba ya yi kira ga mahukunta cewa idan an ciza sai kuma a busa. “Maganar gaskiya ita ce tattalin arzikinmu zai burma wani halin gargara idan aka cigaba da garkame Jihohin nan.”

“Ana samun yawaitar sabawa doka da biyan jami’an tsaro cin hanci domin shiga wurare, har ma da aikata manyan laifuffuka iri-iri. Babu wanda ya san yaushe za a ga karshen wannan.”

Shugaban NLC ya kara da cewa: “Mu na tsoron lamarin zai cabe idan wannan takunkumi ya zarce wata guda.” Wabba ya jinjinawa gwamnati amma ya bukaci ta duba batun bada agaji.

NLC ta bukaci gwamnatin ta fadada rabon wadannan kayan agaji ga sauran Bayin Allah da su ke cikin matsi a sakamakon wannan annoba. Kungiyar ta nemi gwamnati ta nemi Masana.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel