Karyewar Mai: Jihohi na iya rasa kudin FAAC a Watan Yuni inji Gwamnan Gwamnoni

Karyewar Mai: Jihohi na iya rasa kudin FAAC a Watan Yuni inji Gwamnan Gwamnoni

Ganin yadda farashin gangar danyen mai ya karye sosai a kasuwar Duniya, babu shakka tattalin arzikin Najeriya zai gamu da babban kalubale a cikin ‘yan kwanakin nan masu zuwa.

Shugaban gwamnonin Najeriya, Dr. Kayode Fayemi ya ce watakila gwamnonin jihohi ba za su samu wani kudi daga kason FAAC na gwamnatin tarayya a watan Yuni mai zuwa ba.

Gwamnan na jihar Ekiti wanda shi ne shugaban kungiyar gwamnoni na NGF ya tabbatar da cewa gwamnatin tarayya ta bada umarni a kashe Dala miliyan 150 daga cikin asusun NSIA.

Kayode Fayemi ya ce ministar tattalin arziki da kasafin kudi, Zainab Ahmed ta ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada iznin taba wannan kudi domin a cike gibin da za a samu.

Gwamnan ya yi wannan jawabi ne a lokacin da aka yi hira da shi a wani shirin siyasa a gidan talabijin na Channels TV. An yi wannan hira ne a ranar Talata, 21 ga watan Afrilu, 2020.

KU KARANTA: Gwamnoni sun yi na'am da rufe iyakokin jihohi na kwanaki 14

Karyewar Mai: Jihohi na iya rasa kudin FAAC a Watan Yuni inji Gwamnan Gwamnoni
Fayemi ya na tsoron za a rasa kudin da za a raba FAAC a Yuni
Asali: UGC

“Ba ni da labari ko an saki wannan kudi a cikin sa’a 72 da su ka wuce. Abin da na ji daga bakin ministar shi ne shugaban kasa ya bada iznin a cike gibin kason watan Yuni.” Inji Fayemi.

“Kun ga yadda ake fama da farashin danyen mai a Duniya. Don haka ba ka bukatar a fada maka cewa watakila ba za a samu ko da Naira biliyan 200 da za a raba a cikin watan Yuni ba.”

Dr. Fayemi ya ce: “Mu na maganar watan Yuni ne saboda ana saida mai ne watanni uku kafin lokacin. Saboda haka abubuwa ba su cabe a lokacin da aka saida danyen man a baya ba”

Game da kason na FAAC, gwamnan ya ce ya rage buri daga wannan kudi da ake samu, ya ce: “Mu na da taron FAAC a ranar Laraba, saboda haka za mu ji abin da aka yi a wajen taron.”

Kawo yanzu dai ba mu samu labarin matsayar da aka cin ma a wajen wannan taro ba. Ministar kudi da jami’an gwamnatin tarayya ne su ke zama da kwamishinonin kudin jihohi.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel