Ahmed Musa: Maganar cewa Ni da Iyalina mu na dauke da COVID-19 karya ce

Ahmed Musa: Maganar cewa Ni da Iyalina mu na dauke da COVID-19 karya ce

A jiya Laraba mu ka samu labarin cewa tauraron ‘dan wasa Ahmed Musa ya musanya jita-jitar da ke yawo cewa ya na cikin wadanda su ka kamu da cutar nan ta Coronavirus.

Rade-radi su na yawo cewa gwaji ya nuna tsohon ‘dan wasan gaba na kungiyar Leicester City ya na dauke da cutar COVID-19, har ana jita-jitar cewa cutar ta kama na-kusa da shi.

‘Dan wasan na Super Eagles Ahmed Musa ya fito ya yi karin haske bayan ya dawo daga kasar Saudi Arabiya inda ya ke taka leda. Musa ya dawo gida Najeriya ne tare da iyalinsa

Musa ya bayyana cewa shi da iyalin na sa da danginsa za su kauracewa mutane kamar yadda aka saba. ‘Dan wasan kwallon kafan zai shafe kwanaki akalla 14 a killace a cikin gidansa.

Kamar yadda rahotanni su ka bayyana, Ahmed Musa ya shigo Najeriya ne daga kasar Saudi inda mutum 12, 000 su ka kamu da wannan cuta. Musa ya yi hayar wani jirgin sama ne har gida.

KU KARANTA: 'Dan wasan Ingila ya kira 'Yan mata gida yayin da ake zaman kulle

‘Dan wasan mai shekaru 27 ya yi jawabi a shafinsa na Instagram: “Labari ya zo gare ni cewa wasu mutane sun zabi su rika yada labaran karya cewa an gano ina da da cutar COVID-19.”

“Wannan annoba ta ci dubban mutane, don haka abin takaici ne ace wasu mutane su na so su yi amfani da wannan dama domin su samu mabiya a shafukansu ta hanyar yada karya.”

“Ni da iyalina mun shigo daga Saudi Arabiya, kuma mun zabi mu bi dokar gwamnati na killace kanmu na tsawon kwanaki 14, ba wai don mu na dauke da kwayar cutar nan ba.” Inji sa.

Musa ya ce: “Mu na nan garau, ba mu dauke da cutar nan. Ka da ku biyewa masu yada labaran kage game da ni ko iyali na. Ku kare kanku, ku rika bada tazara a cikin bainar jama’a.”

Musa wanda ya ke buga kwallo a kungiyar Al Nasr ya dawo gida ne tare da mai dakinsa da wasu da Legit.ng ta ke kyautata zaton cewa tsohonsa ne da tsohuwarsa da kuma ‘yanuwansa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel