Jahar Borno ta sake babban rashi: Mahaifin tsohon gwamnan jahar ya rasu sanadiyar gobara

Jahar Borno ta sake babban rashi: Mahaifin tsohon gwamnan jahar ya rasu sanadiyar gobara

- Mahaifin tsohon gwamnan jahar Borno, Ali Modu Sheriff ya rasu

- Marigayi Sheriff ya rasu ne a ranar Alhamis, 22 ga watan Afrilu, sakamakon gobara da ta tashi a gidansa da ke hanyar Damboa a Maiduguri

- Zuwa yanzu dai ba a bayyana abun da ya haddasa gobarar ba, sannan iyalansa ba su sanar da batun mutuwar nasa ba kai tsaye

Allah ya yi wa mahaifin tsohon gwamnan jahar Borno, Ali Modu Sheriff rasuwa sanadiyar gobara.

Marigayi Sheriff ya rasu ne a ranar Alhamis, 22 ga watan Afrilu, sakamakon gobara da ta tashi a gidansa da ke hanyar Damboa a Maiduguri, jaridar Premium Times ta ruwaito.

Marigayin ya kasance Galadiman masarautar Borno.

Majiyoyi na kusa da ahlin sun bayyana cewa Sheriff, wanda ke fama da lalura da ke da nasaba da tsufa, bai yi nasarar fita daga gobarar ba, wacce ta afku da misalin karfe 3:00 na tsakar dare.

Jahar Borno ta sake babban rashi: Mahaifin tsohon gwamnan jahar ya rasu sanadiyar gobara
Jahar Borno ta sake babban rashi: Mahaifin tsohon gwamnan jahar ya rasu sanadiyar gobara
Asali: Twitter

Lamarin ya afku ne a lokacin da ake cikin yanayi na hana shige da fice a Maiduguri da sauran yankunan jahar Borno na tsawon kwanaki 14, sakamakon annobar COVID-19.

Zuwa yanzu dai ba a bayyana abun da ya haddasa gobarar ba.

Koda dai iyalansa ba su fitar da kowani jawabi game da mutuwar marigayin ba, sakonnin ta’aziyya na ci gaba da bullowa a shafukan soshiyal midiya na yaran mamacin.

Gwamnatin jahar ba ta aika sakon ta’aziyya ba tukuna. Amma, hadimin gwamnan jahar a kan harkokin labarai, Isa Gusau, ya bayyana mutuwar Mista Sheriff a matsayin babban rashi ga jahar.

Mista Gusau ya ce mutuwar marigayi Abba Kyari, tsohon Shugaban ma’aikatan Shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda ya rasu bayan ya kamu da cutar COVID-19, da na Mista Sheriff wanda ya rasu a gobara, na daga cikin wadanda Musulunci ta bayyana a matsayin ‘shahada’.

A wani jawabi da ya wallafa a shafin Facebook, Mista Gusau ya ce manyan jiga-jigan Bornon guda biyu sun mutu sakamakon annoba wanda ya ce alamu ne na rahmar Allah.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel