Za a dauki lokaci mai tsawo ana fama da annobar coronavirus - WHO

Za a dauki lokaci mai tsawo ana fama da annobar coronavirus - WHO

- Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce za a ci gaba da fama da cutar coronavirus a duniya na tsawon lokaci

- Shugaban hukumar Tedros Adhanom Ghebreyesus ne ya bayyana haka a taron manema labarai a ranar Laraba

- Ya ce yanzu an fara samun saukin cutar a yammacin Turai, amma a Afirka ta tsakiya da kudancin Amurka cutar kara bazuwa ta ke

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta bayyana a ranar Laraba, 22 ga watan Afrilu, cewa annobar coronavirus na ta bazuwa a wasu yankunan Afrika ta tsakiya da kudancin Amurka.

Ta yi gargadin cewa ya zama dole a kula sosai wajen bude hanyoyin shige da fice na duniya.

Shugaban hukumar, Tedros Adhanom Ghebreyesus ne ya bayyana haka a taron manema labarai a ranar Laraba, jaridar Vanguard ta ruwaito.

Ya ce har yanzu cutar na da ban tsaro, amma irin matakan da aka dauka na hana fita da hana taron jama'a ya taimaka wajen dakile bazuwar cutar a kasashe da dama.

Za a dauki lokaci mai tsawo ana fama da annobar coronavirus - WHO
Za a dauki lokaci mai tsawo ana fama da annobar coronavirus - WHO
Asali: Facebook

“Shigar annobar nan a matakin farko a mafi akasarin kasashe, sannan wasu kasashen da ya fara aukawa suna fuskantar dawowar cutar ,” in ji Ghebreyesus

“Kada a rudu, muna da dogon tafiya gabanmu. Wannan annobar za ta dauki tsawon lokaci a tare da mu,” cewarsa, yayin da ya ke sanar da samun saukin cutar a yammacin Turai.

KU KARANTA KUMA: Bayanin Ganduje a kan rahoton yawaitar mutuwar jama'a a Kano

Babban jigon WHO, Dr Mike Ryan, ya yi gargadi a kan bude hanyoyin shige da fice na duniya da wuri, cewa hakan zai bukaci kula na musamman wanda ke cike da hatsari.

A wani labari na daban, mun ji cewa dukkan gwamonin jihohin Najeriya 36 su ka amince da kaddamar da dokar kulle kasa baki daya har na tsawon sati biyu domin dakile yaduwar annobar covid-19.

Gwamnonin, a karkashin kungiyar gwamnonin Najeriya (NGF), sun cimma wannan matsaya ne bayan sauraron bayanai daga gwamnonin jihohin Lagos, Bauchi, Oyo da Ogun.

Shugaban kungiyar NGF, gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi, ne ya fitar da wannan sanarwa bayan kammala taron gwamnonin da aka gudanar ta hanyar amfani da fasahar kiran waya mai nuna bidiyo.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng