Abdallah ya fi dacewa ya zama Shugaban ma’aikatan fadar Buhari – Inji Kpodoh

Abdallah ya fi dacewa ya zama Shugaban ma’aikatan fadar Buhari – Inji Kpodoh

Richard Kpodoh, wanda ya na daya daga cikin wadanda su ka kafa jam’iyyar APC mai mulki, ya sa baki game da wanda ya kamata ya zama sabon shugaban ma’aikatar fadar shugaban kasa.

Cif Richard Kpodoh ya ce Abdulrahaman Abdallah ya na cikin wadanda su ka fi kowa dacewa da rike mukamin na shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari.

Ganin irin cancantarsa ne Kpodoh ya roki shugaba Muhammadu Buhari ya nada Alhaji Abdulrahaman Abdallah a matsayin wanda zai maye gurbin da Abba Kyari ya bari a Aso Villa.

A cewarsa, wannan Bawan Allah Abdulrahaman Abdallah da ya fito daga yankin Malumfashi da ke kudancin jihar Katsina, ya na da abin da ake bukata na zama babban hadimin shugaban kasa.

Kpodoh ya ke cewa Abdulrahaman Abdallah ya nuna rikon amana da rashin son abin Duniya da kuma sadaukar da kai a wurin aikinsa. Jagoran na APC ya ce Abdallah ya yi aikin gwamnati.

KU KARANTA: Abin da ya sa ake yi wa Abba Kyari fatan ya dace da Aljannah

Abdallah ya fi dacewa ya zama Shugaban ma’aikatan fadar Buhari – Inji Kpodoh

Kpodoh ya ba Buhari shawarar wanda zai nada Shugaban ma’aikatan fada
Source: UGC

Fitaccen ‘dan siyasar ya ce Abdallah mutum ne wanda ya ke da ilmin boko sosai, har ma ya yi karatu tare da tsohon shugaban kasa marigayi Ummaru Musa ‘Yaradua wanda ya rasu a 2010.

Babban jigon a jam’iyyar APC a yankin Kudancin kasar, Cif Kpodoh ya ce an taba yi wa wannan mutumi tayin irin wannan kujera a gwamnatin da ta shude, amma ya ki karbar mukamin.

Kamar yadda Kpodoh ya shaidawa ‘yan jarida a garin Fatakwal, jihar Ribas, Abdulrahaman Abdallah ya ki karbar wannan tayi da gwamnati ta yi masa ne saboda wasu dalilan gashin kansa.

"Abdallah ma’aikacin gwamnati ne wanda ya san aiki kuma masanin harkar tattalin arziki, domin ya kai mukamin sakataren din-din-din a ma’aikatar kudi a jihar Katsina.” Inji Kpodoh.

“Mutane da yawa sun san Abdallah cewa mutum ne mai nagarta. Ya na da kwazon aiki, da gaskiya, da yin daidai. Mu na addu’a shugaban kasa Buhari ya zabe shi a wannan kujera.”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel