El-Rufa'i ya saka sabuwar doka a Kaduna bayan warkewarsa daga cutar covid-19

El-Rufa'i ya saka sabuwar doka a Kaduna bayan warkewarsa daga cutar covid-19

A ranar Laraba ne rahotanni su ka bayyana cewa gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufa'i ya warke daga cutar coronavirus.

El-Rufa'i ya wallafa a shafinsa na sada zumunta (tuwita) cewa ya warke daga cutar covid-19 bayan sakamakon gwaji ya nuna cewa ba ya dauke da kwayar cutar yanzu.

Gwamnan ya bayyana cewa iyalinsa sun shiga cikin matsananciyar damuwa yayin da sakamakon gwaji ya nuna cewa ya na dauke da kwayar cutar.

A cewar El-Rufa'i, bayan an killace shi na kusan sati hudu, sakamakon gwajin kwayar cutar da aka sake yi ma sa har sau biyu ya nuna cewa yanzu ya rabu da ita.

Ya rubuta, "ina godiya ga Allah bisa tausayi da jin kansa. Ina godiya ga dumbin jama'ar da su ka tausaya min tare da yi min addu'o'in samun sauki.

"Iyalina sun shiga damuwa, ba don kawai su na tsoron zan iya mutuwa ba, saboda su ma za su iya kamuwa da kwayar cutar ta dalilin mu'amala da ni.

"Iyalina sun bani dukkan goyon bayan da nake bukata, hakazalika abokaina; daga ko ina a fadin duniya, sun aiko min sakonnin dubiya da addu'o'in samun waraka."

A cikin wani jawabin da ya sake fitarwa, El-Rufa'i ya ce ba ya yi wa kowa fatan ya kamu da cutar covid-19.

"Wannan annoba barazana ce ga bil'adama da rayuwa da tattalin arziki.

El-Rufa'i ya saka sabuwar doka a Kaduna bayan warkewarsa daga cutar covid-19
Gwamna El-Rufa'i
Asali: Facebook

"A matsayina na wanda ya taba kamuwa da wannan cuta, ba na yi wa wani fatan ya kamu da ita, koda kuwa makiyina ne," a cewarsa.

Da ya ke jaddada bukatar a hada kai domin yakar cutar covid-19, El-Rufa'i ya ce dole jama'a su yi biyayya ga matakan kare kai da dakile yaduwar annobar.

DUBA WANNAN: Gwamnati ta rufe asibitin da Abba Kyari ya mutu a Legas

El-Rufa'i ya ce akwai bukatar sadaukarwa da inganta tsaftar jiki da ta muhalli tare da kauracewa taron jama'a domin samun galaba a kan annobar cutar covid-19.

"Zan rufe jawabina da sanar da mutanen jihar Kaduna cewa na zo da sabuwar dokar bukatar jama'a su saka takunkumin fuska yayin da za su fita daga gidajensu a kan kowanne dalili.

"Gwamnati za ta samar da takunkumin rufe fuska ga talakawa da ma su karamin karfi. Hakan zai taimaka wajen kare kowa da kowa da kuma dakile yaduwar cutar," a cewarsa.

Gwamnan ya jaddada muhimmancin kauracewa taron jama'ar da yawansu ya kai 10, zama a gida tare da yawan wanke hannu da sabulu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel