Hon. Dabo ya rubutawa Majalisa takarda game da tashin farashin kaya
Wani ‘dan majalisar dokikin jihar Kaduna, Suleiman Ibrahim Dabo ya aikawa majalisar tarayya takarda a game da yadda farashin kaya su ke yin sama a lokacin annobar COVID-19.
Honarabul Suleiman Ibrahim Dabo ya turawa shugabannin majalisar Najeriya takarda, inda ya jawo hankalinsu a kan hauhawan farashin kaya da ake samu a daidai wannan marra.
Sulaiman Dabo wanda ke wakiltar mazabar Zariya a majalisar dokokin Kaduna ya bayyana cewa ya zama dole ayi magana a kan yadda kayan amfani da magunguna su ke ta kara kudi.
Daily Trust ta ce Dabo ya rubuta wannan wasiku ne ga shugaban majalisar dattawa watau Sanata Ahmad Lawan da kuma takwaransa na majalisar wakilai Rt. Hon. Femi Gbajabiamilla.
Rahoton ya bayyana cewa Honarabul Dabo ya yi wa wannan wasika taken: “Tashin farashin kayan amfanin gida da magunguna a lokacin zaman kullen annobar cutar COVID-19”
KU KARANTA: 'Dan Majalisa Kaduna, Dabo da aka yi garkuwa da shi ya samu 'yanci
Dabo wanda shi ne shugaban kwamitin kasafi da tsare-tsare a majalisar Kaduna ya roki majalisar kasar ta gurfanar da shugaban hukumar FCCPC mai kare hakkin masu sayayya a kasuwa.
Tun ba yau ba Legit.ng Hausa ta samu labarin cewa Honarabul Sulaiman Dabo ya sha alwashin yin bakin kokarinsa a game da yadda kaya su ke yi wa Bayin Allah tsada a kasuwanni.
A ranar 24 ga watan Maris ne aka rufe majalisun Najeriya saboda annobar COVID-19. Amma ana sa ran a sake bude majalisar domin a tattauna game da gyaran da za ayi wa kasafin kudi.
Binciken da mu ka yi ya nuna cewa wasu kaya sun kara kudi a kasuwa a ‘yan makonnin nan. Wannan ya zo daidai da lokacin da ake fama da COVID-19 da kuma gabatowar azumi.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng