Cutar COVID-19: Gwamnatin Jiha a Amurka ta kai kasar Sin kara a kotu

Cutar COVID-19: Gwamnatin Jiha a Amurka ta kai kasar Sin kara a kotu

Gwamnatin jihar Missouri a Amurka ta kai karar kasar Sin a kan lamarin annobar COVID-19. Wannan mataki da jihar Amurkar ta dauka ya jawo mata fushi daga mahukuntar kasar Sin.

Jihar Missouri ta na neman kasar ta Sin ta biya ta wasu makudan kudi da sunan jefa ta cikin hadari da ta yi.

Jihar ta zargi Sin da kin yin abin da ya dace wajen tsaida annobar COVID-19.

Jaridar Daily Trust ta ce Duniya ba taba jin labarin irin wannan tuhuma a kotu ba.

Jihar ta shigar da wannan kara ne a lokacin da majalisar Amurka ke kiran a hukunta gwamnatin kasar Sin.

Ta kuma zargi Sin da boye kayan kula da masu jinyar COVID-19 tare da yi wa Duniya karya.

Wasu ‘yan majalisar tarayyar su na ganin cewa akwai hannun Sin wajen barkewar annobar Coronavirus.

A wani bangaren, ana sukar shugaba Donald J. Trump da cewa ya yi sakaci.

Jam’iyyar Republican mai mulki ce ta ke rike da jihar Missouri don haka ba ayi mamaki sosai da aka ji gwamnatin jihar ta shigar da karar kasar Sin a gaban babban wani kotun tarayya ba.

KU KARANTA: Likita ya kamu da Coronavirus yayin duba duba Maras lafiya a Ekiti

Cutar COVID-19: Gwamnatin Jihar Amurka ta kai kasar Sin kara a kotu
Rikicin Amurka da kasar Sin a kan Coronavirus ya kai Kotu
Asali: Getty Images

“Gwamnatin Sin ta yi wa Duniya karya game da hadari da yanayin karfin kwayar cutar COVID-19, tare da hana masu yi wa jama’a shela yin magana.” Inji kwamishinan shari’ar Missouri.

Babban lauyan jihar ta Missouri, Eric Schmitt, ya kara da cewa: “(Kasar Sin) ta kuma ki yin abin da ya dace na hana yaduwar cutar. Dole a hukuntasu a kan danyen aikin da su ka yi.”

Missouri ta gabatar da karar ne ta hanyar tuhumar jam’iyyar gurguzun da ke mulki a Sin. Jihar ta Missouri ta yi korafin cewa za ta iya rasa biliyoyin daloli a sakamakon wannan annoba.

Gwamnatin Missouri ta ce Sin ta nuna halin ko-in-kula game da hakkin jama’a. Lauyan jihar Amurkan ya ce kasar Sin ta rika dakile duk wani labari game da cutar a lokacin da ta fito.

Kasar Sin ta bakin kakakin ma’aikatar kasar wajenta mai suna Geng Shuang, ta karyata wannan zargi. Shuang ya ce gwamnatin Sin ba ta taba boye wani abu game da wannan annoba ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng