Fargabar kamuwa da cutar corona ya sa Likitoci sun bari wata mata ta mutu a Enugu

Fargabar kamuwa da cutar corona ya sa Likitoci sun bari wata mata ta mutu a Enugu

An yi zargin cewa tsoron kamuwa da cutar coronavirus ya sanya wasu likitoci a asibitin koyarwa na jami'ar Enugu sun bari wata mata ta riga mu gidan gaskiya.

Fargabar kamuwa da annobar corona wadda ta zama ruwan dare ta sanya wasu likitoci sun haifar da mutuwar wata mata uwar 'ya'ya hudu.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, matar mai shekaru 35 ta riga mu gidan gaskiya bayan da likitoci sun kauracewa duban lafiyar ta domin gudun kamuwa da cutar corona.

Mijin wannan mata, Nwachukwu Alagbu mai shekaru 40 a duniya, ya bayyana damuwa kwarai da gaske dangane da sakacin da ma'aikatan lafiya suka yi wajen ceto ran mai dakinsa.

Mista Alagbu ya ce sakacin likitoci da sauran ma'aikatan lafiya na asibiti ne yayi sanadiyar mutuwar matarsa.

Ya zargi likitocin asibitin da laifin kisan matarsa a sanadiyar fargaba ta gudun kamuwa da cutar coronavirus.

Ma'aikatan Lafiya a bakin aiki na dakile yaduwar cutar corona
Ma'aikatan Lafiya a bakin aiki na dakile yaduwar cutar corona
Asali: UGC

Sai dai ya zuwa yanzu hukumomin asibitin ba su ce uffan ba game da wannan zargi.

Yayin tattara wannan rahoto inda manema labarai suka nemi jin ta bakin jami'in hulda da al'umma na asibitin, Mr Cyril Keleze, ya ce ba shi da ta cewa.

KARANTA KUMA: Coronavirus: Muna rokon Buhari ya kawo dauki jihar Kano - Ganduje

Sai dai babu shakka ya sha alwashin waiwayar manema labaran domin jin ta bakin asibitin a kan wannan lamari.

Mista Alagbu cikin zubar hawaye ya shaidawa manema labarai irin halin ha'ula'i da likitocin asibitin suka jefa matarsa, Mrs Nkiru Alagbu.

Ya ce ta sha fama da rashin lafiyar zuciya wadda ta kamu da ita tun bayan haihuwar dan ta na hudu shekara guda kenan da ta gabata.

Ya kara da cewa, rashin lafiyar ta sanya matarsa ta rika fama da zazzabi, daukewar numfashi, ciwon kirji, kasala, gumi mai yawa da kuma rashin cin abinci.

A halin yanzu an tabbatar da mutane 782 sun kamu da cutar corona a Najeriya yayin da jimillar wadanda suka kamu a duniya baki daya ya kai 2,573,143.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel