Bayani: Yadda faduwar farashin danyen man Amurka zai shafi Najeriya

Bayani: Yadda faduwar farashin danyen man Amurka zai shafi Najeriya

Karo na farko a tarihin cinikin danyen mai nau’in West Texas Intermediate na Amurka, farashinsa ya yi faduwar da bai taba yi ba.

Da misalin karfe 8:22 na ranar Litinin, ana siyar da man Amurkan kan $-37.45 a kowani gangar mai kamar yadda yake a jerin farashin da Bloomberg ta saki.

Yayinda hakan ya kasance mummunan labari ga kasashen da ke samar da mai, ga wasu yan tsirarun tambayoyi da zai taimake ku wajen fahimtar halin da ake ciki.

Bayani: Yadda faduwar farashin danyen mai zai shafi Najeriya
Bayani: Yadda faduwar farashin danyen mai zai shafi Najeriya
Asali: Depositphotos

Tambaya: Me faduwar farashin mai ke nufi?

Amsa: Hanya mafi sauki na bayanin wannan shine cewa yan kasuwa za su biya abokan cikinikinsu a kan siyan kayansu da suka yi

Tambaya: Shin hakan abu mai kyau ne?

Amsa: A’a, ba abu mai kyau bane. Yan kasuwa da kamfanonin mai na faduwa. Hakan na kuma nufin cewa babu sararin da za a ajiye saura idan aka samar da mai da ya zarta.

KU KARANTA KUMA: Coronavirus: An dakatad da sallar jam'i a masallatai a jahar Nasarawa

Tambaya: Shin wannan farashi zai kasance iri daya a fadin masana’antar?

Amsa: A’a, faduwar farashin a kan danyen man fetur din Amurka ne kadai. Kuma, zai shafi Mayu na gaba ne domin kwangilar watan Yuni na nan a kan $22 duk gangar mai sannan na Yuli na a kan $27 duk gangar mai.

Tambaya: Nan gaba? Mai hakan ke nufi?

Amsa: A masana’antar danyen man fetur, masu matatun mai ko sauran masu siya na iya biyan kudi kafin lokaci na danyen maid a za a kai masu a nan gaba. Don haka, yana iya yiwuwa an siyar da wasu na Mayu tun farkon sheka a kan farashi mai tsada da ya kai $50 ko $60, idan abokin ciniki ya sasanta ko kuma ya biya a watan Janairu.

Tambaya: Kenan mai bai riga ya zama mara daraja ba?

Amsa: A’a bai zama ba

Tambaya: Toh ta yaya hakan zai shafi sauran masu samar da mai?

Amsa: Wannan zai zama jan kunne ga kungiyar kasashe masu fitar da man fetur (OPEC) kan yadda munin bukata ya kai.

Tambaya: Toh ya yake game da farashin danyen mai a Najeriya?

Amsa: Danyen man ya kasance nau’in Brend ne. A yanzu haka, farashin duk gangar danyen mai na Brent na a kan $25.b koda dai yan kasuwan sun ce ana siyar nau’in Najeriya a tsakanin $13 da $15 a baya-bayan nan, farashin bai riga ya shiga tsarin faduwar ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel