COVID-19: Babu darasin tafsiri da jami’in sallar tarawihin azumin nan, Inji Sultan

COVID-19: Babu darasin tafsiri da jami’in sallar tarawihin azumin nan, Inji Sultan

Ganin yadda annobar cutar COVID-19 ta addabi Najeriya da sauran kasashen Duniya, Sarkin musulmi ya bayyana cewa ba za ayi ibadan da aka saba a azumin wannan shekarar ba.

Mai alfarma Sultan Sa’ad Abubakar III ya aika sako zuwa ga musulman Najeriya ganin cewa azumi ya gabato.

A wannan sako, Sultan ya sanar da haramta karatun tafsiri a shekarar nan.

Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III ya kuma bayyana cewa ba za a taru a masallatai domin yin sallar tarawih watau asham a bana ba. Wannan karon musulmai za su yi sallah ne a gidajensu.

Sarkin Muslmin wanda shi ne Shugaban kungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI), ya ce za su yi koyi da sauran kasashen musulmai don haka jama’a ba za su yi wasa da rayukansu wajen ibada ba.

“A matsayinmu na musulmai, ba mu manta da cewa mutuwa riga ce ga kowa ba, amma duk da haka ba za mu yi ganganci da rayuwarmu ba. Suratul Baqarah ta yi mana bayanin haka.”

KU KARANTA: COVID-19: Akwai sauran jan aiki har yanzu Najeriya - Sakataren Gwamnati

COVID-19: Babu darasin tafsiri da jami’in sallar tarawihin azumin nan Inji Sultan Sa'ad
Sultan Sa'ad Abubakar ya ce ba za ayi tafsiri da sallar tarawihin Azumi ba
Asali: Twitter

Jawabin ya ce: “Jama’atu Nasril Islam a karkashin mai alfarma Muhammad Sa’ad Abubakar, ta na taya musulmai murnar karasowar azumin watan Ramadan. Ramadan wata ne na Al-Kur’ani da addu’o’i da ambaton Allah, kuma wata ne na zakkah da sadaka da daren lailatul qadr."

“Amma ganin yadda annobar cutar COVID-19 da ta barke, dole al’ummar musulmai su bi sannu da wannan cuta. Ya kamata a sani cewa dama ya fi kyau a yi sallolin nafila wadanda su ka hada da tarawih a gida, duk da cewa mustahabbi ne yin su a cikin jami’i.” Inji kungiyar JNI.

JNI ta ce: "Karshen takaitawa dai, ba za ayi tafsirin shekara-shekara na azumi ba, kuma babu sallar jami’in tarawihi a masallatai, sai zuwa lokacin da abubuwa su ka dawo daidai.”

Don haka, Sarkin musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar ya umarci kowa ya yi sallah a gida tare da iyalinsa har sai zuwa lokacin da annobar ta lafa, domin gudun yada cutar Coronavirus.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng