Yanzu nan: Cif Richard Akinjide ya cika ya na da shekaru 88

Yanzu nan: Cif Richard Akinjide ya cika ya na da shekaru 88

Richard Akinjide wanda ya na daga cikin manyan dattawan Najeriya ya riga mu zuwa gidan gaskiya. Wannan labari ya zo mana ne da safiyar yau Talata, 21 ga watan Afrilu, 2020.

Wani tsohon ministan Najeriya, Femi Fani-Kayode ya na cikin wadanda su ka fara tabbatarwa Duniya da mutuwar Richard Akinjide wanda ya rasu ya na da shekaru 88 da haihuwa.

Femi Fani-Kayode ya bayyana hakan ne a shafinsa na Tuwita da sanyin safiyar nan.

Tsohon ministan ya yi wa marigayin addu’a, ya na mai cewa kasar Yarbawa da ma Najeriya ta yi babban rashi.

“Babanmu Cif Richard Akinjide, ministan ilmi a jamhuriyya ta farko, ministan shari’a a jamhuriyya ta biyu, ‘dan kishin kasa kuma dattijo ya cika. Ina yi wa iyalinsa addu’a.”

Ana kyautata zaton an haifi marigayin ne a shekarar 1932 a garin Ibadan da ke jihar Oyo. Richard Akinjide ya bar Najeriya ne inda yayi karatun sakandarensa da ilmin shari’a a Landan.

KU KARANTA: Babu maganar canza sunan Jami'a zuwa Abba Kyari - Gwamnatin Imo

A shekarar 1955, Akinjide ya zama Lauya a ketare, daga baya ya dawo Najeriya ya fara aiki. Firayim Minista Abubakar Tafawa-Balewa ya fara nada Akinjide a matsayin ministan ilmi.

Bayan dawowar farar hula a shekarar 1979, marigayi tsohon shugaban kasa Shehu Shagari ya nada Akinjide a matsayin ministan shari’a kuma babban lauyan gwamnatin tarayyar kasar.

Mai ba shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara a kan harkar siyasa watau Babafemi Ojudu, ya tabbatar da wannan labari maras dadi na mutuwar dattijon a shafinsa na Facebook dazu.

Idan ba ku manta ba, ‘diyar marigayin watau Olajumoke Akinjide ta taba rike kujerar minista. Goodluck Jonathan ne ya nada Olajumoke a matsayin karamar ministar birnin tarayya.

Marigayi Richard Akinjide babban lauya ne wanda ya kai matakin SAN. Ya na cikin wadanda su ka yi aikin shirya kudin tsarin mulkin kasar. Da su ne kuma aka kafa jam’iyyar NPN.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel