Kungiya ta sauke Limamin da ya bi dokar Gwamnatin Kaduna, ya garkame Masallaci a Zariya

Kungiya ta sauke Limamin da ya bi dokar Gwamnatin Kaduna, ya garkame Masallaci a Zariya

Shugaban kungityar Jama’atu Izalatil Bid’a Wa’iqamatis Sunnah (JIBWIS) na karamar hukumar Zariya a jihar Kaduna, Sheikh Sani Yakubu ya tsige wani limami da ke karkashinsa.

Rahotanni sun bayyana cewa Sani Yakubu ya sauke Malam Abubakar Sarki-Aminu daga Limanci ne saboda ya yi wa gwamnatin jihar Kaduna da’a wajen kin gudanar da sallolin yini.

Abubakar Sarki-Aminu ya kasance Limamin da ke bada sallolin yini a masallacin Juma’ar Sheik Abubakar Mahmood Gumi da ke unguwar Kofar Gayan Low-cost a cikin garin Zariya.

Wannan dattijon malami ya shafe kusan shekaru 40 ya na limanci a masallacin. Sai dai kin gudanar da sallah har da ta Juma’a kamar yadda aka saba ya jawo ya rasa limancinsa.

A watan Maris ne gwamnatin Kaduna a karkashin Nasir El-Rufai ta haramta duk wata haduwar da za ta tara mutum akalla 50 a wuri guda, wannan doka ta shafi haduwa a wuraren ibada.

KU KARANTA: Coronavirus ta sa za ayi wa ‘Yan Majalisa gibi a albashinsu

Kungiya ta sauke Limamin da ya bi dokar Gwamnatin Kaduna, ya garkame Masallaci a Zariya

Gwamnan Kaduna ya dakatar da salloli bayan bullar COVID-19
Source: UGC

Wannan mataki da hukuma ta dauka ya sa limamin ya guji tsaida salloli a masallaci. Shugaban JIBWIS wanda aka fi sani da Izala, ya tabbatar da cewa kungiyar ta sauke limamin na ta.

Yakubu bai yi wa ‘yan jarida karin bayani game da wannan mataki da kungiyar JIBWIS ta dauka ba, sai dai ya ce Alhaji Shehu Dan-Maikuli zai yi magana game da lamarin a madadinsa.

Da aka tuntubi Alhaji Shehu Dan-Maikuli game da abin da ya sa aka sauke limamin, sai ya ce matsalolin su na da yawa, sai dai kawai ya ayyano wasu daga cikin zunubansa a takaice.

Dan-Maikuli ya ce Marigayi Sheik Usman Baban-Tune ya taba sulhunta kwamitin masallacin da wannan limami, amma duk da haka Imam Sarki-Aminu bai bi dokokin da aka gindaya ba.

Malam Dan-Maikuli ya ce wata rana kwatsam limamin ya sanar za a daina sallar jami’i ba tare da tuntubar kwamitinsu ba. A dalilin wannan aka tsige shi, aka nada Malam Ahmad Tijjani.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel