Yanzu Yanzu: Yan Boko Haram sun kai hari Geidam

Yanzu Yanzu: Yan Boko Haram sun kai hari Geidam

- Mayakan kungiyar Boko Haram sun kaddamar da hari a karamar hukumar Geidam da ke jahar Yobe

- Mayakan sun kai farmaki garin ta kudancin kauyen Gumsa dazun nan, sannan suka yi ta harbi ba kakkautawa

- Harin na zuwa ne yan sa’o’i kadan bayan rundunar sojin sama na Operation Lafiya Dole sun kashe manyan shugabannin Boko Haram da dama

A yanzu haka wasu da ake zargin yan kungiyar Boko Haram ne, suna kaddamar da hari a karamar hukumar Geidam da ke jahar Yobe, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Harin na zuwa ne yan sa’o’i kadan bayan rundunar sojin sama na Operation Lafiya Dole sun kashe manyan shugabannin Boko Haram da dama.

Yanzu Yanzu: Yan Boko Haram sun kai hari Geidam

Yanzu Yanzu: Yan Boko Haram sun kai hari Geidam
Source: Twitter

Wasu majiyoyi a Geidam sun tabbatar da cewar, mayakan sun kai farmaki garin ta kudancin kauyen Gumsa dazun nan, sannan suka yi ta harbi ba kakkautawa.

Ya ce mutane na ta gudu domin tsira, yayinda maharan suka shigo a daidai lokacin da mazauna yankin suka fita don gudanar da harkokinsu.

Mazauna garin sun shiga damuwa domin wannan ne karo na farko da yan ta’addan ke kai hari Geidam da safe.

KU KARANTA KUMA: An yi wa Abba kyari sadakar uku da ta bakwai a Borno (hotuna)

A wani labarin, mun ji cewa Abubakar Shekau yana tunanin yadda makamai tare da mika kansa ga gwamnatin Najeriya, majiya mai karfi ta sirri daga yankin Arewa maso gabas din kasar nan ta sanar da jaridar The Vanguard.

Majiyar ta sanar da jaridar cewa, Shekau ya fara neman hanya mai sauki don mika kanshi ga gwamnatin.

Kamar yadda majiyar tace, shugaban Boko Haram din ya fara tuntubar wasu kungiyoyin taimakon kai da kai na kasashen duniya don samun ragwame daga gwamnatin Najeriya.

"Ina tsammanin Boko Haram ta kusa zuwa karshe don Shekau na kokarin mika kansa ga hukumomi a Najeriya.

"Ya kagara kuma akwai tabbacin cewa tsananta harin da dakarun kasar nan ke kai musu ne ya kawo hakan," majiyar tace.

Majiyar ta kara da cewa, a kwanakin nan dai kungiyar Boko Haram din na fuskantar kalubale mai tarin yawa sakamakon saka su gaba da dakarun sojin kasar nan suka yi.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel