Malaman Jami’a sun zargi Gwamnatin Tarayya da yi masu mugun horo da yunwa

Malaman Jami’a sun zargi Gwamnatin Tarayya da yi masu mugun horo da yunwa

A daidai lokacin da jama’a su ke jimamin halin da annobar COVID-19 ta jefa Najeriya da wasu kasashen Duniya, kungiyar malaman jami’a ASUU ta na nuna cewa abin ya hadu mata da yawa.

Kungiyar ASUU ta bayyana cewa gwamnatin tarayya ta na horarsu da yunwa a lokacin nan da ake ciki na annoba. Jaridar Punch ta fitar da wannan rahoto a ranar Lahadi, 19 ga watan Afrilu.

ASUU ta ce da ace gwamnatin Najeriya ta yi irin hobbasan da ta ke yi yanzu a harkar lafiya wajen ceto sha’anin ilmi, da yanzu an ga karshen yajin aikin da ake ta fama da shi a jami’o’in kasar.

Shugaban wannan kungiya ta ASUU, Farfesa Biodun Ogunyemi ya ce idan da gwamnati za ta maida hankali a kan ilmi kamar yadda ake yakar annobar COVID-19, da sai an ga banbanci.

Farfesa Biodun Ogunyemi ya ke cewa yajin aikin ASUU ba zai zarce lokacin wannan annoba idan da gwamnati ta yi da gaske.

Tun a karshen watan Maris, ASUU ta tafi yajin sai-baba-ta-gani.

KU KARANTA: NCDC ta yi kuskure wajen tara alkalamun masu dauke da COVID-19

Malaman Jami’a sun zargi Gwamnatin Tarayya da yi masu mugun horo da yunwa

Babban Ministan harkar ilmin Najeriya Mallam Adamu Adamu
Source: Facebook

Biodun Ogunyemi ya ke fadawa ‘yan jarida cewa: “Gwamnati ta jagwalgwala lamarin. A cikin watanni biyun nan, ba a biya ‘ya ‘yanmu da ke jami’o’in gwamnatin tarayya albashi ba.”

“Kun hana mutane albashinsu, kuma ku na tunanin za su koma bakin aiki hankali kwance.”

“A lokacin da ake bada tallafi ga mutane, ka na hana dubban mutane hanyar samun abincincu, kuma ka na tunanin ka na shawo kan matsala ne, ka kulla yaki ne da Malamai masu ilmi.”

“Saboda haka kamar wannan gwamnati ta shirya yaki ne da ASUU da ‘ya ‘yanta. Babu wanda ya damu da walwalar iyalin wadanda aka jefa cikin wani hali a sakamakon zaman kulle.”

“Mutane sun shiga halin ha’ula’i, ba su da wurin zuwa, kuma ka na amfani da yunwa domin ka azabtar da su, wannan kisan kare dangi ne.” ASUU ta ce akwai bukatar a waiwayi ilmi.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng News

Online view pixel