Katsina: Rayuka sun salwanta bayan 'yan bindiga sun kai hari a wasu kauyuka
- Ana tsammanin mutane da yawa ne suka rasa rayukansu a kananan hukumomin Safana, Danmusa da Dutsinma na jihar Katsina
- Hakan ta faru ne bayan da 'yan bindiga suka kai wa jama'ar yankin hari don samun abincin da gwamnati ta kai musu tallafi
- Mazauna kauyen sun mayar da martani, lamarin da yasa 'yan bindigar masu tarin yawa suka fada wa 'yan kauyen da kisa
Ana tsammanin mutane masu yawa sun rasa rayukansu sakamakon harin da ‘yan bindiga suka kaiwa kananan hukumomi 3 a jihar Katsina.
Kananan hukumomin sun hada da Safana, Danmusa da Dutsinma.
Majiyoyi sun ce an kai harin ne kwanaki kadan bayan an kai kayan tallafi tare da raba wa ‘yan sansanin gudun hijira da ke yankin.
Maharan sun je ne bayan mutane sun kammala karbar tallafin da gwamnati ta basu da safiyar ranar.
Maharan sun kwace kayayyakin abincin tare da yin awon gaba dasu.
Mazauna kauyen sun fara fada da maharan, lamarin da yasa ‘yan bindigar suka kara fitowa da yawansu don fin karfi ga mazauna kauyen.
Kamar yadda jaridar Daily Trust ta bayyana, wata majiya ta sanar da cewa an mika gawawwaki da yawa zuwa asibitin yankin.
“A halin yanzu da nake magana, ana ci gaba da kai harin”, majiyar tace.
A yayin da aka tuntubi rundunar ‘yan sandan jihar, basu ce komai ba game da harin da aka kai.

Asali: Twitter
DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: An fara sallar jana'izar Abba Kyari a Abuja
A wani labari na daban, an sake samun mutum biyu dauke da cutar coronavirus a jihar Katsina. Wannan ne ya kai jimillar masu cutar zuwa 9 a jihar kamar yadda hukumar hana yaduwar cututtuka (NCDC) ta bayyana.
Shugaban kwamitin yaki da coronavirus na jihar Katsina, Mannir Yakubu, ya sanar da hakan a yau Juma'a da yammaci yayin zantawa da manema labarai a gidan gwamnatin jihar Katsina.
Jaridar The Nation ta bayyana cewa, NCDC ta wallafa a shafinta na twitter cewa an samu mutum bakwai dauke da cutar a jihar a ranar Alhamis.
Amma kuma a yau Juma'a, an sake samun wasu mutum biyu dauke da cutar tare da tarin mutanen da suka yi mu'amala dasu. Tuni dai an ganosu tare da daukar samfur don gwaji.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng