Najeriya ta samu sassaucin biyan bashi daga China da kasashen G-20

Najeriya ta samu sassaucin biyan bashi daga China da kasashen G-20

Kasar China da kasashen G-20, sun amince su dakatar da karbar basukan da suke bin kasashe matalauta a duniya, wadanda bankin duniya ya yi wa lakabi a matsayin kasashe masu tasowa.

A taron watan Afrilu 2020 da ke gudana na babban bankin duniya da asusun lamuni na duniya wato IMF, David Malpass, shugaban bankin duniya, ya ce daga farkon watan Mayu, za a dakatar da karban bashi.

“Kasashe matalauta za su samu sassauci daga ranar 1 ga watan Mayu. Ta haka, za su iya mayar da hankali ga arzikin kasarsu wajen yaki da annobar COVID-19 da kuma tattalin arzikinsu.

“Na lura cewa a taron G-20, kasar China na goyon bayan yarjejeniyar kasa da kasa na sassauta wa kasashe masu tasowa bashi idan suka nemi ayi hakuri.

“Hakan na da matukar muhimmanci saboda China na daya daga cikin manyan kasashen da ke bin bashi, kuma kasancewarsu a cikin wannan kokari na da muhimmanci kuma abun maraba ne.”

Najeriya ta samu sassaucin biyan bashi daga China da kasashen G-20
Najeriya ta samu sassaucin biyan bashi daga China da kasashen G-20
Asali: Facebook

Kasashen da ke karkashin kungiyar kasashe masu tasowa a duniya (IDA) sune wadanda kudaden shigarsu ke kasa da $1,175.

Kasashe kamar su Najeriya da Pakistani, sun kasance kasashe masu tasowa da suka cancanta, duba ga matakin kudaden shigarsu, sannan kuma sun kasance wadanda ke da damar ranto kudade. Ana masu lakabi da ‘kasashen da suka cancanci a basu bashi'.

Malpass ya ce za a kafa wani tsari da zai dunga lura da yadda kasashe masu tasowa ke amfani da kudaden da aka bayar bashi na rage radadi.

KU KARANTA KUMA: Abba Kyari: Atiku ya yi martani a kan mutuwar shugaban ma’aikatan shugaban kasa

“Don haka idan gwamnati ta tara kudi ta hanyar rashin biyan wadanda ke binta bashi, toh ana sanya ran cewa za su yi amfani da kudaden wajen habbaka fannin lafiya, ilimi, habbaka tattalin arziki, ayyuka da kuma hanyoyin taimaka wa mutanen kasar su,” in ji shi.

Ya kuma ce tsarin zai tabbatar da cewar kasashe masu tasowa sun samu karin kyauta da basussukan yarjejeniya.

Ba a sanar da cikakken bayani kan yarjejeniyar sassauta karban bashin ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel