An kashe mutum uku yayinda yan iska suka kai hari wani gari a Abuja

An kashe mutum uku yayinda yan iska suka kai hari wani gari a Abuja

Wasu miyagu, a ranar Alhamis, 16 ga watan Afrilu, sun kai hari kauyen Peace da ke yankin Lugbe, babbar birnin tarayya, inda hakan ya yi sanadiyar mutuwar mutane uku. An kuma lalata dukiyoyi da dama.

Mazauna yankin sun bayyana lamarin a matsayin karamin fashi da ya rikida ya zama babba a garin.

An tattaro cewa lamarin ya afku ne lokacin da mazauna yankin suka yiwa wasu matasa duka, bayan sun dakile yunkurin fashi da yaran suka so aiwatarwa, sannan sai suka sake su daga baya.

Daga bisani sai yaban, suka shirya wasu gugun yan uwansu inda suka farma garin, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

An tattaro cewa an kashe uku daga cikin maharan, sannan mazauna yankin da dama sun jikkata. An kona gidaje da motoci, yayinda aka fasa gilashin gaban wasu motocin.

An kashe mutum uku yayinda yan iska suka kai hari wani gari a Abuja
An kashe mutum uku yayinda yan iska suka kai hari wani gari a Abuja
Asali: Twitter

Yan sanda daga yankin ofishinsu na Lugbe sun yi gaggawan zuwa wajen faruwar lamarin, sannan aka dawo da zaman lafiya a yankin.

Da aka tuntube shi, kakakin yan sandan birnin tarayya, DSP Anjuguri Manzah ya tabbatar da lamarin.

Ya ce ana kan bincike, yayinda aka tsaurara matakan tsaro a yankin.

A wani labarin kuma, mun ji cewa akalla mutane 6 ne suka gamu da ajalinsu a hannun gungun miyagun yan bindiga a wasu kananan hukumomin jahar Neja guda biyu, da misalin karfe 10 zuwa 12 na ranar Laraba.

Daily Trust ta ruwaito yan bindigan sun kashe mutane 5 a karamar hukumar Shiroro yayin da wasu da dama suka jikkata a harin, a garin Madaki, karamar hukumar Rafi inda suka kashe 1.

Yan bindigan da yawansu ya kai mutum 50 sun kutsa kai cikin kauyen Manta ne a kan babura suna harbin mai kan uwa da wabi, a dalilin haka fiye da mutane 600 suka tsere daga gidajensu.

Yan banga sun yi kokarin karawa da yan bindigan, amma sai suka ga wani jirgi mai saukan angulu yana biye dasu, don haka suka ranta ana kare don tsira da ransu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng