Yan bindiga sun yi garkuwa da wani Malamin Musulunci a Jigawa

Yan bindiga sun yi garkuwa da wani Malamin Musulunci a Jigawa

- Hukumar yan sandan jahar Jigawa, ta tabbatar da sace wani malamin addinin Musulunci a garin Ringim, da ke karamar hukumar Ringim na jahar

- Wasu yan bindiga su biyar a kan babura ne suka kai farmaki yankin, sannan suka waske da Malamin

- Kakakin yan sandan jahar ya bayar da tabbacin cewa ana kan bincike cikin lamarin

Rundunar yan sandan jahar Jigawa, ta tabbatar da sace wani malamin addinin Musulunci a garin Ringim, da ke karamar hukumar Ringim na jahar, jaridar The Nation ta ruwaito.

Kakakin yan sandan jahar, SP Abdu Jinjiri, ya tabbatar da lamarin ga manema labarai a garin Dutse, babbar birnin jahar Jigawa.

Yan bindiga sun yi garkuwa da wani Malamin Musulunci a Jigawa

Yan bindiga sun yi garkuwa da wani Malamin Musulunci a Jigawa
Source: UGC

Ya ce “wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba, kimanin su biyar sun kai mamaya gidan, sannan suka sace malamin mai suna Malam Sani Sale a garin Ringim.”

Ya yi bayanin cewa “lamarin ya faru a ranar 17 ga watan Maris, inda yan bindigan suka zo kan babura guda uku sannan suka je gidan mutumin da ke kauyen Kulawa da ke karamar hukumar Ringim, inda suka tafi dashi.”

A cewarsa, jim kadan bayan sun samu labarin, sai suka tura tawagar yan sanda zuwa wajen da abun ya faru.

KU KARANTA KUMA: Sakamakon gwajin mutane 90 da ke nuna alamun COVID-19 a Abuja ya fito, basa dauke da cutar

Ya kara da cewar yan bindigan sun fitar da malamin daga kauyen kafin su iso. A halin da ake ciki a yanzu, an kama mutane biyu da ke da nasaba da lamarin.

Jinjiri ya bayar da tabbacin cewa ana kan bincike cikin lamarin.

A wani labarin kuma mun ji cewa, wasu 'yan bindiga sun yi awon gaba da mata ma su jego guda uku a kauyen Karaukarau da ke karamar hukumar Giwa a jihar Kaduna.

Wani mazaunin kauyen mai suna Malam Sani Bakali ya shaidawa wakilin jaridar 'The Nation' cewa 'yan bindigar, dauke da muggan makamai, sun fara yunkurin tafiya da mata 13 daga kauyen.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel